Atiku Ya Ce A Dawo Da Tsoffin Sojoji Da Suka Yi Ritaya Domin Yakar Ta'addanci

 


Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dawo da tsoffin hafsoshin soji a matsayin mafita ga kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Atiku Abubakar, wanda shi ma tsohon dan takarar shugaban kasa ne, ya yi wannan kiran ne a cikin wata sanarwa a kan "tabarbarewar yanayin tsaro" a ranar Talata kamar yadda RFI Hausa ta labarto.

Atiku Abubakar yace “yanayin tsaro a Nijeriya yana tabarbarewa cikin sauri kuma talakawan Najeriya suna rayuwa cikin fargaba game da rayukansu da na‘ yan uwansu. Babu inda ake da kwanciyar hankali, kama daga Gonaki da kasuwanni da makarantu cikin gidaje da masallatai, majami'u, da kuma birane duk abin ya shafa.

Atiku Abukar ya kara da cewa: “Yan ta’adda na ci gaba da fafada yankunansu sama da Arewa maso gabas, zuwa yankuna masu nisa har zuwa jihar Neja a Arewa ta tsakiya, mai nisan ‘yan tafiyar sa’o’i daga Babban Birnin Tarayya"

Tsohon mataimakin shugaban kasar yace, "Yanzu lokaci ya yi da za a yanke hukunci game da shugabanci, inda ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi la’akari da tuna daukacin tsoffin sojoji maza da mata, wadanda ke da niyyar komawa bakin aiki, domin taimakawa dakarun dake fafatawa da ayyukan tsageru ta kowane kusurwa, har sai sun samu nasara.

Nijeriya Nada Gwarazan Tsoffin Sojoji

Ya ce, a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kwamitin tsaro na kasa, "yana sane da cewa Najeriya tana da dimbin gwarazan tsoffin sojoji, wadanda suka samu horo a gida da waje kuma har yanzu suna nan da ransu".

Ya ce babu wani amfani na barin wannan damar ta sukurkuce, alhali kasa na cikin wani yanayi.

Post a Comment

0 Comments