Wasu Majiyar Zuma Times Hausa da ta hada da Mujallar Fim sun bayyana cewa tsofafin jarumai na Kannywood, Sani Danja da Mansura Isa sun d...
Wasu
Majiyar Zuma Times Hausa da ta hada
da Mujallar Fim sun bayyana cewa
tsofafin jarumai na Kannywood, Sani Danja da Mansura Isa sun dade da rabuwa
inda Mansura ta koma gidan haya da zama tare da 'ya'yanta hudu.
An
ce dalilin rabuwarsu na da alaka da auren sirri da Sani Danja ya yi a Kaduna ba
tare da sanin Mansura ba har sai da matar ta haihu.
Majiyar
ta ci gaba da cewa Mansura ta yi alkawari ba za ta ba shi ko daya daga cikin ‘ya’yan
ba.
Wadanda
ke kusa da Mansura sun bayana cewa ba wannan ne farko da Sani Danja da Mansura
suka rabu ba don ko a baya ya taba sakinta.
Zuma
Times Hausa ta samu karin bayani da ke cewa Mansura ta gaji da halayen mijinta
ne don yadda ya sake mata hidimomin gida inda ta ke daukar dawainiyyar tafiyar
da al'amuran gidan.
Bincike
ya nuna cewa Mansura dai mace ce mai kokarin neman na kanta da taimakawa marasa
karfi.
Duk
kokarin da majiyar ta yi ta don jin na bakin ma'auratan ya ci tura.
Ubangiji Allah Ya kyauta, Allah Ya qara la'antar shedan la'ananne wanda bai qaunar sunnar Manzon Allah (SAW).
ReplyDelete