Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BARAZANAR EL-RUFAI GA MALAMAN JAMI'A: Harbin Iska Ka Kake Yi -Martanin ASUU

Daga Muhammad Haruna MADOGARA ta labarto cewa; kungiyar Malaman Jami'o'i reshen Jami'ar jihar Kaduna, ASUU ta maida...Daga Muhammad Haruna

MADOGARA ta labarto cewa; kungiyar Malaman Jami'o'i reshen Jami'ar jihar Kaduna, ASUU ta maida martani mai gauni ga Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai bisa barazanar da ya yi na korar Malaman Jami'ar jihar Kaduna wato KASU bisa shiga yajin aiki da suka yi biyo bayan umurnin kungiyar kwadago ta kasa, NLC. 

Kungiyar ta ASUU ta maida martanin ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar Kwamared Peter Adamu da kuma Sakatare Kwamared Silas Ibrahim Akos reshen KASU suka sanyawa hannu, suka kuma fitar a ranar 18 ga watan Mayun 2021. 

MADOGARA ta labarto cewa; a cikin sanarwar kungiyar ta ASUU ta ce domin ilmantar da al'umma, ya kamata su sani cewa; ayyukan Malaman Jami'ar sune ilmantarwa ta hanyar karantarwa. Sai kuma bunkasa ilimi ta hanyar bincike da kuma ayyukan jin kai ga al'umma. A cewar ASUU wadannan sune tushen ayyukansu wajen samar da ci gaba a jihar da ma kasa baki daya. 

"Abin mamaki ne da kuma takaici a ce membobin kungiyarmu da suke kwashe lokacinsu rana da dare suna gudanar da ayyukansu ta hanyar duba takardu da bincike amma a ce su koma sanya sunayensu a takardar rijistar zuwa makaranta", inji ASUU. 

ASUU ta nemi membobinta da ka da su tsorata da matakin na gwamna El-Rufai, kuma su yi watsi da batun rijistar sunayensu; "abin da ke faruwa yanzu dama ce na dawo da martabar dokokin da suka kafa jami'ar da sauran matsalolin da suka addabi Jami'ar", suka tabbatar. 

ASUU ta ci gaba da cewa; "barazanar korar membobinmu harbin iska ce kawai, kuma ba zai yi aiki ba. Domin ma'aikata na da na su hanyoyin hukunta mutum wanda ke cikin dokokin Jami'a. Ya kamata membobin mu su sani cewa barazanar (gwamnan) tuni aka sanar da manyan jami'an da suka kamata na babbar kungiyarmu, kuma sun tabbatar da cewa suna tare damu. Sun yi alkawarin shiga lamarin cikin lokaci", ASUU ta tabbatar. 

A karshe ASUU ta nemi membobinta da su jajirce da kuma sadaukar wajen kwatar 'yanci domin tabbatar da adalci. 

          Kwafin takardar da ASUU ta fitar. 

No comments