Barazanar NNPC Ba Zai Hana Mu Biyan Mafi Karancin Albashi Na 30, 000 Ba –Gwamna Badaru Na Jigawa

 


Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubuakar ya ce jiharsa na da kudin da za ta iya biyan ma'aikatanta duk da barazanar NNPC na cewa ba zai bayar da kosisi ba daga asusun tarayya da da ake rabawa jihohi kamar yadda BBC ta labarto.

Gwamnan ya ba da tabbacin ne yayin da yake yi wa ma'aikata jawabi a dakin taro na Ahmadu Bello da ke Dutse babban birnin Jihar, a wani bangare na bikin ranar ma'aikata ta duniya.

Sannan ya tabbatar wa da ma'aikata jajurcewarsa na biyan naira 30,000 a matsayin mafi karancin albashi a watanni masu zuwa duk da barazanar da kamfanin mai na NNPC ya yi cewa ba zai saka kudi a asusun gwamnatin tarayya ba a wata mai zuwa.

"Ma'aikata su kwantar da hankalinsu za mu biya su albashinsu kamar yadda aka saba kuma akan lokaci".

"An sha zargina da boye kudi ba tare da kashe su ba, amma mu mun san irin wannan lokacin yana zuwa, kuma ga shi ya zo," a cewarsa.

"Lokacin da muka zo mun san wammam lokacin na zuwa da ba za mu samu komai ba daga gwamnatin tarayya saboda faduwar farashin mai, bugu da kari annobar korona ta kara jefa tattalin arzikin kasar cikin wani mawuyacin hali" in ji Badar

Post a Comment

0 Comments