Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Bayan Ayyana Shi Ruwa A Jallo, Ayuba Wabba Ya Jagoranci Zanga-zanga Zuwa Gidan Gwamnatin Kaduna

  Daga Ammar Muhammad Wakilinmu dake cikin masu zanga-zangar da kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) ta shirya a Kaduna, ya labarto ma...

 
Daga Ammar Muhammad

Wakilinmu dake cikin masu zanga-zangar da kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) ta shirya a Kaduna, ya labarto mana cewa; shugaban kungiyar ta NLC, Kwamared Ayuba Wabba a halin yanzu yana jagorantar membobin kungiyar zanga-zangar zuwa gidan gwamnatin jihar Kaduna. 

Wannan Zanga-zangar ya biyo bayan sanarwar da gwamna Nasir El-Rufai ya fitar na cewa yana neman shugaban kungiyar kwadago ruwa a jallo da sauran wasu bisa zarginsu da 'durkusar da tattalin arzikin' jihar da kuma 'lalata kayayyakin gwamnati'. 

Wakilin namu ya shaida mana cewa; daruruwan jama'a masu zanga-zangar wanda Wabba ke jagorantarsu sun bi ta titin Waff Road a Kaduna inda suka nufi gidan gwamnatin jihar. 

No comments