Kwana daya bayan da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya amince da kuskuren da kasarsa ta tafka a kisan kiyashin Rwanda, a karon farko ka...
Kwana daya
bayan da shugaban Faransa Emmanuel Macron ya amince da kuskuren da kasarsa ta
tafka a kisan kiyashin Rwanda, a karon farko kasar Jamus ta amince da aikata
kisan kare dangi a Namibia a lokacin mulkin mallaka, inda ta yi alkawarin ba da
tallafin kudi na sama da Yuro biliyan daya a matsayin diyya ga kasar dake Kudancin
Afirka.
Turawan
mulkin mallaka na Jamus sun kashe dubun dubatar kabilun ‘yan asalin Herero da
Nama a wani kisan gillar da aka yi a shekarun 1904-1908 - wanda masana tarihi
suka yi wa lakabi da kisan kare dangi na farko a karni na 20 da ya lalata
dangantaka tsakanin Namibia da Jamus tsawon shekaru.
Duk
da yake Berlin ta amince da lallai da sa hannun mahukuntar mulkin mallaka a
ta'asar ta Namibiya, sai dai ta dage kan kin daukar alhaki kai tsaye da kuma watsi
da batun biyan kudin diyya.
AMINCEWA KARON FARKO
To
sai dai cikin sanarwa da ministan Harkokin Wajen Jamus Heiko Maas ya fitar
ranar Juma’a ya ce; “yanzu sun amince tare da ambaton kalmar kisan kare dangi a
hukumance”, inji shi.
Inda
ya yaba da yarjejeniyar fahimtar juna da suka samu bayan kwashe sama da shekaru
biyar suna tattaunawa da Namibia kan abubuwan da suka faru a yankin da Berlin
ta rike daga shekarun 1884 zuwa 1915.
"Dangane
wannan nauyi da tarihi ya nuna, da irin É—abi'a na Jamus, za mu nemi gafara daga
Namibia da zuriyar waÉ—anda aka cutar" don "ta'asar" da aka
aikata, in ji Maas.
BIYAN DIYYA
Ministan
ya ce, domin nuna karamci jamus za ta tallafawa Namibiya da Yuro biliyan daya da miliyan 100 don sake
ginata da ci gaban kasar.
Majiyar
kusa ta yarjejeniyar ta ce, cikin shekaru 30 Jamus za ta biya kudin sannu a
hankali, kuma dole ya soma da zuriyar Hereo da Nama kai tsaye.
-Rahoton
RFI Hausa/MADOGARA
No comments