Bayan Shekara 62 Za A Yi Sallar Idi A Filin Mallawa A Karon Farko A Zariya


Daga Muhammad Farouk

Bayan nadin Ambassada Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin Sarkin Zazzau na 19, a wannan shekarar za a yi sallar Idi a filin Idi na Mallawa dake sabon titin Zariya zuwa Jos. 


Binciken da majiyarmu ta Jaridar Daily Trust ta yi ya nuna cewa kowanne Sarki a masarautar Zazzau suna da filin da suke Jagorantar idinsu wanda filayen ke sassa daban-daban a Zariya. 

Wannan shi ne karo farko cikin shekaru akalla 62 da za a sauya wurin sallar Idi a garin na Zariya sakamakon Sarakuna biyu kafin Sarki Ahmad Nuhu Bamalli sun fito ne daga gidan Katsinawa, inda aka rika gudanar da sallar Idi a filin Idi dake Kofar Doka. 

Da yake tabbatar da labarin, Babban Jami'i (Chief Protocol Officer) ga Sarkin na Zazzau, Alhaji Abubakar Ladan, ya ce sallar Idin na bana zai gudana ne a filin Idin Mallawa. 

Majiyarmu ta Daily Trust ta labarto cewa Sarki Muhammad Aminu, Sarkin Zazzau na 17 wanda ya fito daga gidan Sarautar Katsinawa  ya kwashe shekara 16 yana sarautar Zazzau, kafin Marigayi Sarki Shehu Idris ya kwashe shekara 46 yana sarautar Zazzau a matsayin Sarki na 18. 

Mazauna garin Zariya 'yan kasa da shekaru 70 sun taso ne sun ga ana sallar Idi a filin Idi na Katsinawa dake Kofar Doka. 


Mutane da dama na murna a garin Zariya inda suke dokin zuwan ranar sallah domin su kasance cikin jerin wadanda za su kafa tarihin kasancewa a filin Idi na Mallawa wanda aka kwashe kusan shekara 100 ba a yi sallah a cikinsa ba. 

Post a Comment

0 Comments