BIDIYON DALA: Ja’afar Ja’afar Ya Yi Hijira Zuwa Birtaniya


Fitaccen dan jarida, mawallafin Daily Nigerian, Ja’afar Ja’afar ya tattara inasa-inasa tare da iyalansa gaba ɗaya sun koma kasar Birtaniya da zama har sai ya gamsu babu mai bibiyar rayuwarsa.

A hira da ya yi da PREMIUM TIMES ranar Lahadi, Ja’afar ya bayyana cewa hankalinsa ba a kwance ya ke ba a kullum a kasar nan tun bayan ganowa da ya yi lallai ana farautarsa.

"Ba zan dawo Nijeriya ba sai na samu tabbacin cewa gwamnati za ta samar mini da tsaro da iyalaina da kuma bani dama a matsayina na dan jarida in rika aiki na kamar yadda doka ta bani", ya tabbatar. 

Ja’afar ya shaida wa PREMIUM TIMES a cikin Afirilu cewa rundunar ‘yan sandan Nijeriya na nemansa ruwa a jallo saboda bidiyon da ya wallafa na karbar cin hanci daloli da aka nuna gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na karɓa.

A wata wasika da rundunar ‘yan sandan kasa ta rubuta wa Ja’afar, ta hannu A.A Elleman, dake ofishin Sufeto Janar din Nijeriya, rundunar na bukatar Ja’afar ya bayyana a hedikwatar rundunar ƴan sanda ta kasa, a Abuja domin yin bayani game da wasu korafe-korafe da aka shigar a kansa.

Waɗannan ƙorafe-ƙorafe kuwa sun haɗa da, ɓata suna, yin zagon ƙasa, shirga ƙarya da neman ingiza mutane su tada husuma da keta wa ofishin Sufeto Janar din ƴan sandan Nijeriya rigar rashin mutunci wanda aka samu yana da hannu a ciki.

"A dalilin haka rundunar ta ke buƙatar mawallafin jaridar ya bayyana a ofishinta domin amsa wasu tambayoyi akan waɗannan Zargi". 

Ja’afar ya karyata zargin ƴan sandan.

"Babu abin da ya haɗani da Sufeto Janar din ƴan sandan Nijeriya, ban taɓa wani rubutu akan sa ba na ɓatanci ko tun a baya ma. Rufa-rufa kawai ake yi min, idan na bayyana hedikwatar ƴan sandan sai su damke ni", ya ce. 

Idan ba a manta ba jaridar Daily Nigerian ce ta fara wallafa wasu bidiyo da ke nuna gwamnan Kano Abdullahi Ganduje na karkacewa ya na cusa bandir din daloli a aljihun kaftaninsa.

Ana zargi wadannan kuɗaɗe da gwamna Ganduje ke karɓar su daga hannun wani dan kwangila ne da ya ke mika masa kason sa na cin hancin wata kwangila da gwamnatin jihar ta ba su.

Post a Comment

0 Comments