Biyan Kudin Fansa Ga Masu Garkuwa Da Mutane Haramun Ne - Sheikh Maqari

 


Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan da ke Nijeriya, Farfesa Ibrahim Maqari, ya bayyana cewa biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane haramun ne a Musulunci.

Jaridar Dateline da ake wallafawa a shafin intanet ta ambato malamin, wanda shi ne mataimakin babban limamin Masallacin Juma'a na Abuja, yana cewa Musulunci ya hana mabiyansa bayar da kudin fansa ga makiya da ake yaki da su.

Malamin, wanda ya bayyana haka lokacin Tafsirin da yake gabatarwa a watana azumin Ramadana, ya kara da cewa biyan kudin fansa zai karfafa gwiwar masu garkuwa da mutane da kuma ba su karin kudi da za su sayi makamai don ci gaba da kai hare-hare.

“Tun da Allah (SWT) ya haramta biyan kudi ga makiyi wanda yake yaki da kai, domin kada ka kara masa karfi, don haka biyan kudin fansa domin a saki wanda aka yi garkuwa da shi haramun,” in ji shi.

Malamin ya ambato Hadisin da wani mutum ya je wurin Manzon Allah yana tambayarsa kan abin da zai yi idan wani ya yi yunkurin ya yi masa fashi da makami, inda Annabi (SAW) ya umarce shi da ya yake shi.

Batun biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane dai yana jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin 'yan Najeriya inda wasu ke ganin ya dace a biya domin ceton rai, yayin da wasu ke ganin hakan raguwar dabara ce.

-BBC Hausa


Post a Comment

0 Comments