Dan wasan tsakiya na Manchester United Bruno Fernandes ya lashe kyautar gwarzon gasar Europa ta bana, yayin da Samuel Chukwueze dan asalin...
Dan wasan tsakiya na
Manchester United Bruno Fernandes ya lashe kyautar gwarzon gasar Europa ta
bana, yayin da Samuel Chukwueze dan asalin Najeriya dake Villarreal ya zama dan
wasa na 16 mafi kwazo a gasar UEFA da aka kammala.
Villarreal ta doke
Manchester United ne dai da kwallaye
11-10 a bugun fanareti bayan tashi 1-1 daga wasan da suka fafata a
zangon karshen gasar cin Kofin na Europa a daren ranar Laraba.
Bruno Fernandes da ya
samu maki 9,531 ya ci kwallaye biyar kuma ya taimaka aka ci hudu a wasanni tara
da ya buga wa kungiyar ta Red Devils.
Gerard Moreno na
Villarreal shi ne na biyu da maki 8, 555, yayin da Edinson Cavani na Manchester
United ya zama na uku da maki 8,506.
No comments