Buhari Ya Amince A Kafa Hukumar Takaita Yaduwar Kananan Makamai

 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da a kafa hukumar takaita yaduwar kananan makamai a kasar.

A sanarwar da mai taimaka wa shugaban kasar kan shafukan sada zumunta, Bashir Ahmad, ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar Litinin, ya ambato Kakakin ofishin mai bai wa shugaba Buhari shawara a kan sha'anin tsaro yana cewa hukumar za ta kasance a karkashin ofishin na su.

Hukumar za ta maye gurbin kwamitin shugaban kasa kan dakile yaduwar kananan makamai, in ji sanarwar.

Kafa hukumar "na cikin matakan inganta tsaron Nijeriya domin magance barazanar tsaro da kuma karfafa shirin da kasashen yankin ke yi wajen takaitawa da magance matsalar yaduwar kananan makamai," a cewar sanarwar.

A baya dai Shugaba Buhari ya sha kokawa kan karakainar kananan makamai da ma manya cikin kasar, lamarin da ya ta'allaka da yakin da aka yi a kasar Libya.

Hukumomi sun bayyana cewa akwai dubban kananan makamai a hannun 'yan kasar, abin da ke ta'azzara hare-hare da kuma yin barazana ga zaman lafiyar Nijeriya, BBC ta labarto.

 

 

Post a Comment

0 Comments