Buhari Ya Ce A Binciki Hadiza Bala Kan Zargin Badakala

 


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da umarnin dakatar da shugabar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta ƙasar, wato NPA, Hajiya Hadiza Bala Usman daga muƙaminta, domin a gudanar da bincike game da wasu kura-kurai da ake zargin ta da aikatawa.

An kuma umarci wani jami'i, Muhammadu Koko, ya riƙe muƙaminta, yayin da ake gudanar da binciken, wanda wani kwamiti da aka naɗa karkashin jagorancin darakta mai kula da sufurin jiragen ruwan a ma'aikatar sufuri ta ƙasar, zai gudanar.

Gwamnati ta ce ministan ma'aikatar sufuri ne ya nemi Shugaba Buhari ya ba shi izinin kafa kwamitin bincike don ya duba yadda ake gudanar da ayyuka a fannin jiragen ruwa na Najeriya wanda Hadiza Bala Usman ke shugabanta.

Ya kuma ce yayin da ake wannan bincike ya kamata a dakatar da ayyukanta har zuwa lokacin da za a kammala shi.

A tattaunawarsa da BBC kakakin fadar shugaban ƙasa, Garba Shehu ya ce an dakatar da Hadiza Bala Usman ne saboda "ita ma'aikata tana zargin cewa akwai umarnin da aka bayar da dama wadanda ba a aiwatar da su ba."

Sai dai ya ƙara da cewa idan Allah ya sa ta wanke kanta bayan an kammala bincike, shugaban ƙasar zai ba ta izinin komawa bakin aikinta, kodayake ya ce ba a san lokacin da za a kammala binciken ba.

''Idan ta wanke kanta to shugaban ƙasa zai yi mata adalci ta koma ta ci gaba da aikinta amma idan akwai kura-kurai da aka gano toh ba a san abinda zai biyo baya ba'', in ji Garba Shehu.

Sai dai kakakin bai yi ƙarin haske ba a kan kura-kuran da ake zarginta da tafkawa, amma a cewarsa ma'aikatar sufuri na zargin cewa akwai umarni da dama da aka bayar da ba a aiwatar ba.

A shekara ta 2016 Shugaba Buhari ya naɗa Hadiza Bala Usman a matsayin shugabar hukumar NPA da wasu daraktoci uku da za su yi aiki tare.

Kafin a ba ta wannan matsayi Hadiza ta kasance shugabar ma'aikata ta gwamnan jihar Kaduna.

Kuma ita ce wadda ta kirkiro tare da taka rawa a ƙungiyar nan mai fafutukar ganin an ceto ƴan matan Chibok, wato Bring Back Our Girls, tun lokacin Shugaba Goodluck Jonathan.


Post a Comment

0 Comments