RFI Hausa ta labarto cewa; Gidaje a kauyuka sun fara daraja a Faransa sakamakon yadda ‘yan birni ke turuwar saye saboda ta’azzarar annoba...
RFI Hausa ta labarto cewa; Gidaje a kauyuka sun fara daraja a Faransa sakamakon
yadda ‘yan birni ke turuwar saye saboda ta’azzarar annobar Corona, da kuma
yadda take kara mamayar mutane musamman a cikin birane. Hukumar kula da
kididdiga ce ta bayyana hakan a jiya Alhamis, tana mai cewa tsoron Corona ne ya
tilastawa jama’a komawa kauyuka.
Ta
cikin kididdigar da hukumar ta fitar ta ce ya zuwa yanzu mutane kusan dubu dari
da goma sha daya da dari 930 ne suka sayi gidaje a kauyuka wadanda kuma daga
birane suka koma.
Hukumar
ta ce yawan kudaden da aka kashe wajen sayen gidajen sun kai yuro miliyan 23 da
rabi.
Kasar
Faransa dai na cikin jerin kasashen da suke shan fama da annobar Corona wadda a
shekaraniya Talata ta dakatar da jama’a daga Burtaniya shiga kasar ta don kare
yaduwar cutar.
Hukumomin
kasar sun ce tun bullar cutar a 2019 mutanen birnin suka fara guduwa zuwa
kauyuka don kare kansu daga cutar, amma a bana yafi ta’azzara la’akari da
makudan kudaden da jama’a ke kashewa wajen hada-hadar kudaden.
Cinikayyar
gidaje na kara habbaka saboda wannan dalili, lamarin da ke taka rawa wajen
habbaka tattalin arzikin kasar da ya ke cikin mayuwacin hali saboda annobar
Coronan.
No comments