Dalilan Da Ya Sa Muka Kori Ma'aikacinmu Da Aka Kama Da Matar Aure A Otel -Hisbah

 


Hukumar Hisbah reshen jihar Kano ta sallami Sani Nasidi Uba Rimo, daya daga cikin kwamandojinta da aka yi zargin an kama da matar aure a Otel.

Kakakin hukumar, Lawal Fagge, ya tabbatar da hakan ranar a ranar Talata, Daily Trust ta ruwaito. Ya ce kwamitin da ta gudanar da bincike kan zargin da aka yi masa ta kama shi da laifin da ake zarginsa.

Rimo, ya kasance babban jami'in da yake yaki da karuwai a jihar Kano. Amma an samu mishkila lokacin da aka yi zargin an kama shi da wata matar aure a Sabon Gari, a cikin watan Fabarairu.

Lokacin da aka tambaye shi ko mene ne alakarsa da matar? An ruwaito cewa ya ce matar 'yar'uwarsa ce, kuma ya ajiye ta a Otel ne don ta samu matsala da mijinta.

Dalilin hakan ne kwamanda Janar na Hisbah, Ustaz Harun Muhammad Ibn Sina, ya nada kwamiti don binciken lamarin. Inda daga karshe aka kama shi da laifin da ake zarginsa. 


Post a Comment

0 Comments