Manoma a Najeriya sun ce aikin daminar bana zai fuskanci mummunar barazana fiyeda ta shekarun baya, saboda kalubalen tsaro da kasar ke fama da shi kamar yadda VOA Hausa ta labarto.
Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta Nijeriyar ke cewa, ta horas da matasa da dama kan amfani da fasahar sadarwa ta zamani wajen gudanar da harkokin noma.
Baya ga ayyukan ta’addancin mayakan Boko Haram a yankin arewa maso gabas, matsalar satar mutane domin karbar kudin fansa ita ce ta mamaye yankin yamma na arewaci da kuma yankunan tsakiyar Najeriya da sauran miyagun ayyyukan bata gari.
Kazalika
ayyukan ta’adanci na ‘yan kungiyar IPOB na ci gaba da wakana a yankin kudu maso
gabashin kasar.
Galibin
miyagun ayyukan nan sun fi kamari a yankunan karkara, lamarin da kungiyar
manoman Najeriya ke cewa, ‘ya yan ta ba sa iya zuwa gonakin su domin ayyukan
noma.
Hakan
dai na zuwa ne a dai dai lokacin da hukumar bunkasa ilimin fasahar sadarwa ta
Najeriya NITDA ke cewa, ta horas da dinbin matasa a karkashin shirinta na
bunkasa ayyukan noma ta hanyar amfani da fasahar sadarwa ta zamani.
Sai
dai baya ga kalubalen tsaro, kungiyar manoman ta Nijeriya ta ce akwai matsalar
kidayar manoman kasar da kuma nau’ikan amfanin gona da suke nomawa.
0 Comments