Dan Majalisa Ya Tsira Daga Harin ‘Yan Bindiga A Katsina

 


Daga Muhammad Farouk


Dan majalisar jihar mai wakiltar Batsari, Alhaji Jabiru Yusufu Yau-Yau ya tsallake harin ‘yan bindiga kamar yadda Katsina City News ta labarto

Alhaji Jabiru Yau-Yau ya tsallake harin ‘yan bindigar ne a daidai kauyen Garwa a lokacin da ya je ziyarar ta’aziyyah.

Wakilin Katsina City News ya labarto cewa Alhaji Jabiru Yau-Yau ya ce ‘yan kauyen sun shaida masa cewa ‘yan leken asirin masu garkuwa da jama’ar ne suka shaida musu zuwansa, shiyasa suka zo akan Babura suka tare hanyar da ya shiga kauyen. Wanda hakan ya sanya wadansu ‘yan kauyen da suka ga abin da ya faru suka shaida masa da cewa ya canza hanya idan ya tashi komawa.

A yayin da ‘yan bindigar suka yi zaman jiran dakon Alhaji Jabiru Yau-Yau ya bayyana ta hanyar da suka tare domin su yi garkuwa da shi, ko su kashe shi, amma ba tare da sun sani ba tuni ya sauya hanyar ta daji ya koma inda ya fito tare da rakiyar jami’an tsaron da yake tafe da su.

 

Post a Comment

0 Comments