Dubban Daruruwan Almajiran Shaikh Zakzaky Sun Yi Muzaharar Kudus A Nijeriya

 


Daga Auwal Adam

Kamar yadda suka saba a duk shekara, mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya da aka fi sani da ‘yan shi’a almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun gudanar da muzaharorin nuna goyon baya ga al’ummar Falasdinu kan mamayar da haramtacciyar gwamnatin Isra’ila ke yi musu.

Jerin gwanon na su wanda suka saba yi a duk Juma’ar karshen watan Ramadan, a bana ma sun gudanar da shi a garuruwa da dama da ya hada Kano, Kaduna, Abuja, Zariya, Jigawa, Katsina, Sakkwato, Bauchi, Jos, Nasarawa, da sauran su.

A yayin jerin gwanon na su sun rika wakokin nuna goyon baya ga Falasdinu da la’anta ga Amurka da kuma Isra’ila. Wakilanmu sun labarto mana cewa; a karshen rufe wannan muzaharar an kona tutocin Amurka da Isra’ila a wani mataki na Allah-wadai da abin da Isra’ila ke yi bisa goyon bayan Amurka.

Har wala yau masu muzaharar sun rika raba takarda kan dalilin fitowar na su. Takardar mai taken; ‘YANCI GA KUDUS, ’YANCI GA SHAIKH ZAKZAKY!’, Shaikh Abdulhamid Bello ne ya sanya mata hannu.

Ga cikakken bayanin da takardar ta kumsa kamar yadda suka raba;

‘YANCI GA KUDUS, ’YANCI GA SHAIKH ZAKZAKY!’

A wannan wata na Ramadan, al’ummar musulmi masu kishi sukan shirya tarurrukan gangami da muzaharori na lumana don fadakar da jama’a irin mamayar da Yahudawan Sahayoniya suke yi wa masallacin Kudus mai tsarki. A shekarar 1979, Imam Khomeini ya ayyana ware kowace Juma’ar karshe ta watan Ramadan a matsayin Ranar Kudus, kuma ya yi kira ga Musulmi a duk fadin duniya da su rika yin gangami kan haka. Tun sannan kuma Jagoran Harka Islamiyya, wanda ake tsare da shi a yanzu, Shaikh Ibraheem Zakzaky, ya rika shirya gangami da muzaharori na Ranar Kudus kawo yanzu. To, a yau Ranar Kudus ta zama wata rana da duniya ke hakkakawa. Wannan gangami ya zama wani bangare na gwagwarmayar Musulmi masu kishi don ganin gaskiya da adalci sun tabbata a duniyar da zalunci da rashin bin doka suka mamaye.

Don haka muna kira ga al’ummar musulmi da sauran jama’a masu kaunar gaskiya da adalci a duk fadin duniya su shigo wannan tafiya a yi da su. To, me ya sa? Saboda Kudus ko Jerusalem, tamkar zuciya ce ta Musulunci da al’ummar musulmi. Matsayinta a kowane zamani yana nuna irin kyautatuwar halin da al’ummar Musulmi suke ciki. Su kuwa makiya sukan hari ita wannan zuciya ce a duk lokacin da yanayi ya ba da damar hakan a tsawon tarihi. Ma’ana irin halin mamaya da danniya da Kudus ke ciki a yanzu, shi ne halin da al’ummar Musulmi a kusan duk fadin duniya suke ciki.

Dalili na biyu kuma shi ne, kalmomi ba za su iya cikakken bayanin irin mummunan halin da Palasdinawa suke ciki a Palasdinu da ke karkashin mamayar Yahudawan Sahayoniya. A ‘yan kwanakin nan ma sai da kungiyar kare hakkin dan Adam mai suna HRW a takaice, ta fitar da wani rahoton shekara-shekara, inda ta kara tabbatar da abin da muka dade muna fada a irin wannan gangamin, cewa Jami’an gwamnatin Isra’ila suna aikata laifukan yaki na nuna wariyar addini da danniya, wadanda dukkanin biyun nan laifukan yaki ne ga dan Adam.

A tsawon fiye da gomomin shekaru akwai fassarar kasa da kasa da ta bayyana nuna wariya a matsayin wani laifi idan Jami’an wata hukuma bisa tsari suna danne wata jama’a a wani yanki da suke da iko a kai, kuma suna cin zarafin su da nufin tabbatar da iko a kan jama’ar da ake dannewar don amfanin jama’ar da ke yin danniyar. Don kawo sauyi na gaske, dole mu bayyana lamarin a hakikanin yadda yake: Tsarin Isra’ila wani tsari ne na danniya da nuna wariya wanda kuma bai nuna alamun gushewa ba, wanda kuma a hakikanin gaskiya ya shiga cikin fassarar nuna wariya na addini.

Alal hakika kasashen duniya a tsawon shekaru sun yi ta shashantar da duk wani rahoton danniya daga Palasdinu tare da kau da kai daga lamarin, wanda ake ganin sa a kusan kullum. A halin yanzu fa a kowace rana a yankin Gaza na Palasdinu akan haifi yaro ne tamkar a kurkuku mara rufin sama, in kuma a yankin Yammacin kogin Jordan ne, to ba shi da wasu hakkoki na kowane dan kasa, in kuma a Isra’ila ne, to ana haihuwar sa a matsayin mara daraja a idon doka, in kuma a kasashen da ke ketare ne, to ana haihuwar sa a matsayin dan gudun hijira ne, tamkar iyayensa da kakanninsa, saboda kawai shi Bapalasdine ne ba Bayahude ba.

Lalle kam Harkar Musulunci ta duniya na da sauran jan aiki a gabanta kafin ta kai ga ganin nasarar gwagwarmayar da take yi na ’yanta Palasdinu daga danniya da mamayar Yahudawan Sahayoniya. Amma kafin nan dole sai an samu kasashen Musulmi da dama da suka samu gagarumin sauyi shigen irin wanda Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta samu. Duk ran da aka ce duniyar Musulunci ta dawo da lafiyarta, dole kanwar na ki za ta sa Yahudawan Sahayoniya su nemi sulhun zaman lafiya, kasashen Yammacin Turai su turo jiragen ruwa da na sama don kwashe su daga yankin Palasdinu, ita kuma Amurka ta yi musu tayin ware musu yankunan kasarta inda za su zauna.

A karshe, a yayin da muke wannan muzahara ko gangami, muna kara jaddada kiran da muka shafe shekaru biyar mawuyata muna yi na a saki Jagoranmu, Shaikh Ibraheem Zakzaky, matarsa da sauran ‘yan’uwa maza da mata da ake tsare da su tun bayan kisan kiyashin Zariya da gwamnatin Buharin nan ta aiwatar a Disamban 2015. Shaikh Zakzaky bai aikata laifin komai ba, kamar yadda wata babbar kotun Abuja ta tabbatar tun 2016, don haka a bar shi ya tafi gida a matsayin Malami mai cikakken ’yanci.

SA HANNU

SHAIKH ABDULHAMID BELLO ZARIA

07/05/2021


Post a Comment

0 Comments