Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Duk Likita Da Malamin Jami'ar Da Ya Shiga Yajin Aikin NLC Ya Kori Kansa, Inji El-Rufai

Daga Ammar Muhammad Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gargadi ma’aikatan jinya na asibitoci mallakar jihar da ka da su kusk...Daga Ammar Muhammad

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya gargadi ma’aikatan jinya na asibitoci mallakar jihar da ka da su kuskura su shiga yajin aikin da kungiyar kwadago (NLC) wacce ta fara a Kaduna tun ranar Litinin.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin wata zungureriyar sanarwa da ya fitar a ranar Talata, inda gwamna El-Rufai ya ce duk wadanda aka samu sun shiga yajin aikin, su sani sun sallami kawukansu daga aiki. 

Sannan ya bayyana cewa; hatta albashin ma’aikatan na wannan watan ba za a biya su ba kuma ma za a yi amfani da kudin ne wajen karawa sauran ma'aikatan jinyar da ba su je yajin aikin ba su yi lamuran rayuwarsu. 

Haka zalika ya zargi wadansu ma'aikatan jinya da yunkurin kashe wani jariri wanda a cewarsa ma'aikatan jinyar (nas-nas) sun janye na'urar shakar iskar da ke tallafawa jaririn. Wanda gwamnan ya ce; tuni aka mikawa ma'aikatar Shari'a ta jihar sunayen ma'aikatan jinyar domin daukar matakin da ya dace a kan su ja yunkurin kisan kai. Inda ya ce wasu ma'aikatan lafiyar ma sun ki duba marasa lafiya da gangar saboda sun tsunduma cikin yajin aikin da NLC ta fara. 

Haka zalika sanarwar ta gwamna El-Rufai wanda Kakakinsa, Muyiwa Adeyeke ya sanyawa hannu, duk Malamin Jami'ar jihar Kaduna wato KASU da ya ki zuwa aiki, shi ma ya sallami kan shi. 

Wannan gargadi, bai tsaya ga nas-nas da likitoci ba har da ma’aikatan hukumomin gwamnatin jihar sai da gwamnan ya doka musu gargadi. 

AN SA ZARE TSAKANIN NLC DA EL-RUFAI

Duk da shelar gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, na neman shugaban NLC Ayuba Wabba ruwa a jallo, kwatsam sai aka gan shi da dandazon 'yan kungiyar Kwadago sun hau titi da safiyar yau Talata zuwa gidan gwamnatin jihar Kaduna.

NLC dai ta tabbatar da cewa za ta yi zanga-zanga har na tsawon kwana biyar a jihar Kaduna domin tsayar da komai cik har sai gwamnan ya sauya matsayarsa kan ma'aikatan jihar. 

Sai sai gwamna Nasir El-Rufai ya nemi taimakon al'ummar Kaduna domin bada bayanan yadda za a kama shugaban kungiyar Kwadago Ayuba Wabba, inda ya zarge shi da sauran 'yan kungiyar kwadago da laifin 'durkusar da tattalin arzikin jihar' da kuma 'kai wa kayayyakin gwamnati' hari.

El-Rufai ya ce yajin aikin da Wabba ya kira a jihar Kaduna, ya saba wa doka, saboda haka gwamnati na neman da a cafke shi, kuma duk wanda ya bada bayanan inda yake ko ya yi sanadiyyar aka kama shi za a bashi kyautar kudi mai tsoka.

A zanga-zangar ta yau Talata wacce ta fara daga NEPA Roundabout dake cikin garin Kaduna, wakilin MADOGARA ya labarto cewa wasu 'yan jagaliya sun afka wa masu zanga-zanga a daidai shataletalen kamfanin na NEPA a Kaduna. Sai dai 'yan sanda sun tarwatsa su da tiya gas. 

No comments