FALLASA: Yadda Aka Kashe Naira Miliyan 56 Wajen Gyaran Dakunan Dalibai A ABU Zariya

 


Daga Muhammad Farouk

Tracka Nigeria, wani shiri a karkashin BudgIT da yake bai wa ‘yan kasa damar su binciki ayyukan da aka yi a cikin al’ummarsu, ya bankado wani aiki da aka yi almundahana wanda gwamnatin tarayya ta yi kasafin naira miliyan 56 domin gyara dakunan dalibai na ICSA/Ramat Hostel dake Jami’ar Ahmadu Bello dake Zariya, a jihar Kaduna . 

Kasafin aikin wanda aka sanya shi a cikin jerin kasafin kudin jihar Kaduna na 2020 an sanya shi a matsayin aikin da yake gudana kamar yadda majiyarmu ta FIJ ta wallafa.

 “na je dakunan daliban domin binciken aikin, wanda aka sanya shi a matsayin yana gudana. Da na isa dakunan, sai na tarar rufin dakin ne kawai aka gyara”, kamar yadda Jami’in TrackaNG Bright Osula ya shaidawa FIJ.

Ya ci gaba da cewa; “abin da suka yi bai kai kudin da aka ware wa aikin ba. A cikin dakunan dalibai komai ya lalace. Kamar aikin na jiran ruwa ya zo ya yi awon gaba shi”, ya labarta. 

Dalibai da dama da majiyarmu ta samu damar tattaunawa da su sun koka bisa lalacewar dakunan kwanan na su na ICSA/Ramat na Jami’ar, inda suka shaidawa Bright cewa abin da yake da kyau kawai a dakunan shi ne wutar lantarki da suka samu, amma ba ya ga haka ba abin da suke samu mai kyau. 

“an gudanar da aikin gyaran dakunan ne wata uku da ya gabata”, ini Osula ya shaidawa FIJ. “akalla wata daya ko biyu ya isa a gyara dakunan. Abin da na gani rashin kyakkyawan shugabanci ne”, ya jaddada. 

Wani aikin da aka fitar da kasafinsa a gyara a Jami’ar shi ne wani rumbu da aka ware masa naira miliyan 19, kuma aka sanya masa; “aikin yana gudana”. Sai dai mai lura da rumbun ya ce ba abin da aka taba yi wa rumbun na gyara cikin sama da shekara 30.

“ba a taba ko taba rumbun ba”, ya tabbatar.

Bayanai sun nuna cewa da zarar damina ta sauka, dalibai za su jigata sakamakon rashin yin aikin yadda ya kamata. Saboda da yawan tagogin dakunan ba a gyara su ba baya ga rufin da aka gyara wanda TrackNG ta ce bai cancanci a ce an kashe wannan kudin wajen gyaran rufin kawai ba. 


Ga wasu hotunan cikin dakunan daliban; 

Post a Comment

0 Comments