Shugaban rukunin Jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN) da kuma Franco-British International University d...
Shugaban rukunin Jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN) da kuma Franco-British International University dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya taya abokinsa, Mr John Mkunu murnar zagayowar ranar haihuwarsa a yau Alhamis 6 ga watan Mayun 2021.
Mkunu shi ne Darakta a bangaren hada-hadar ci gaban kasuwanci ta Afrika a Jamesh Investment dake birnin Cape Town a kasar Afrika ta Kudu.
Farfesa Abubakar Gwarzo a cikin sakon taya murna da ya sanyawa hannu da kansa kuma ya rabawa manema labarai daga birnin Paris, ya taya Mkumu murnar karin shekara daya a duniya, inda ya bayyana shi a matsayin aboki kuma mai kishin Afrika
Mu'assasin Jami'ar ta MAAUN ya yi nuni da cewa nahiyar Afrika tana alfahari da Mkumu bisa yadda ya yi nasarar kafa ma'aikatu da masana'antun kasuwanci a kasarsa ta Afrika ta Kudu.
A cewar Farfesa Abubakar Gwarzo, John Mkumu ya iya mu'amala da al'umma musamman abokan huldar kasuwancinsa da masu kawo masa ziyara.
"Ina son amfani da wannan dama na taya ka murna bisa zagayowar ranar haihuwarka. Allah ta'ala ya karo wadansu shekarun masu yawa cikin koshin lafiya da za su taimaka wajen gudanar da wadansu kyawawan ayyukan da kake yi wajen ci gaban Afrika", inji shi.
Ya ci gaba da cewa; "Mr John Mkumu a yanzu haka yana zaune a garin Cape Town dake Afrika ta Kudu, abokina ne, duk lokacin da na ziyarci kasar yana ba ni kulawa ta musamman. A bisa haka ina matuka godiya gare shi", inji Farfesa Abubakar Gwarzo.
Har wala yau shugaban rukunin Jami'o'in, ya bayyana John Mkumu a matsayin mutumin da ya bada gudummawa wajen ci gaban bangaren ilimi, wanda ya ce dukkanin Jami'o'i a fadin duniyarnan ya kamata su san irin yadda yake taimakawa bangaren.
A cewarsa, Mkumu ya kafa turaku mai muhimmanci a nahiyar Afrika ta hanyar kulla alakar kasuwanci da kuna gwamnatoci da sauran su al'umma.
No comments