Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Farfesa Gwarzo Ya Taya Shugabar LWA, Madeleine Mkumu Murnar Ranar Haihuwarta

Shugaban rukunin Jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN) da Franco-British International University, dake Ka...Shugaban rukunin Jami'o'in Maryam Abacha American University (MAAUN) da Franco-British International University, dake Kaduna, Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, ya taya shugaba kuma wacce ta kafa Kamfanin 'Leading Women Africa', Mrs Madelein Mkunu murnar zagayowar ranar haihuwarta. 

Mrs Mkunu ta kasance jagora ce ta duniya da take fafutikar ci gaban harkokin mata, da kuma huldar kasuwanci da horaswa wacce take zaune a birnin Cape Town ta kasar Afrika ta Kudu. 

Farfesa Abubakar Gwarzo a sakon taya murnar da ya sanyawa hannu kuma ya rabawa manema labarai a Kano a ranar Alhamis, ya bayyana Mrs Mkunu a matsayin 'yar kasuwa mai hangen nesa wacce ta samarwa da fasaharta da tunaninta mutunci, tare da daukar matakai cikin natsuwa da suka shafi mata da kuma ci gaban kasuwanci a Afrika. 


Shugaban rukunin Jami'o'in na MAAUN har wala yau ya taya ta murna bisa yadda  ta rungumi harkokin kasuwanci da ci gaban mata kuma ta kasance Darakta ta LWA, wani kamfanin zuba hannun jari da yake mayar da hankali wajen karfafa yawan adadin mata a harkokin zuba hannun jari, kasuwancin duniya, da sauran wadansu ayyuka a nahiyar Afrika. 


"Ina son amfani da wannan dama wajen taya ki murna a wannan rana ta zagayowar ranar haihuwarki. Allah ta'ala ya karo wadansu shekarun cikin koshin lafiya domin samun damar kawo ci gaba a harkokin kasuwanci da kuma samar da tsare-tsaren da za su kawo ci gaban mata a nahiyar Afrika", inji shi. 


Haka zalika ya karkare da cewa; "Kamfanin LWA a cikin shirye-shiryensa da ayyukansa ya yi nasarar hada alaka tsakanin mata 'yan kasuwa na nahiyar Afrika da sauran nahiyoyin duniya, wannan ya sanya nake taya shugaba kuma wacce ta samar da wannan kamfani murnar zagayowar ranar Haihuwarta", inji Farfesa Abubakar Gwarzo. 

No comments