FCE Zariya Ta Rage Kudin Karbar Satifiket Daga Dubu Sha Uku Zuwa Dubu Biyar


Daga Wakilinmu

Kwalejin horar da Malamai ta gwamnatin Tarayya dake Zariya (FCE, Zariya) ta rage kudin da ake karba a yayin da dalibin da ya kammala makarantar ya zo karbar shaidar kammalawa. 

Sanarwar rage kudin ta bayyana ne a ranar 21 ga watan Afrilun 2021 inda ma'ajin makarantar, Dr M. S. Uwaisu ya sanyawa hannu. 

Dr M. S. Uwaisu ya nemi dalibai da sauran al'ummar makarantar da su lura da wannan sauyin da aka samu da Mukaddashin shugaban makarantar ya kawo domin saukakawa daliban wajen karbar Satifiket din na su. 

Dr M. S. Uwaisu ya har wala yau ya nemi wadanda suka samu matsala da su tuntubi ofishin ma'ajin kudin makarantar domin yin bayani. 


Post a Comment

0 Comments