Gwamna Ganduje Ya Yi Ƙarin Shekarun Aiki Da Ritaya Ga Malaman Boko Na Kano


Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya ƙara wa malaman jihar shekarun aiki da shekarun da ya kamata su yi ritaya.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ofishinsa ya fitar, inda ya ƙarawa malaman jihar shekaru biyar na aiki daga shekara 35 zuwa 40, haka ma shekarun ritaya daga 60 zuwa 65.

Gwamnan ya sanar da matakin hakan ne a wani bikin karramawa na ƙungiyar ƙwadago NLC a albarkacin bikin ranar ma’aikata da aka yi a ranar Asabar 1 ga watan Mayu.

Gwamnan Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya ɗauki matakin ne domin ƙarfafa malaman da kuma ilimi. 

Gwamnan ya ce matakin ya shafi dukkanin malaman Firamare da Sakandare da na gaba da Sakandare.

A wasu ƙasashe na duniya ma’aikata kan yi zanga-zanga kan tsawaita wa’adin shekarun ritaya ko na aiki.

Post a Comment

0 Comments