Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Matawalle Ya Jagoranci Ayyukan Tsaro Tare Da Bankado Maboya Da Kuma Kama Sanannen Mai Kai Hare-hare

Daga Fatima Idris Gwamnan jihar Zamfara, Dakta Bello Mohammed Matawallen Maradun ya jagoranci wata tawagar jami'an tsaro ind...Daga Fatima Idris

Gwamnan jihar Zamfara, Dakta Bello Mohammed Matawallen Maradun ya jagoranci wata tawagar jami'an tsaro inda suka bankado matsugunan wasu shahararrun 'yan bindiga masu kai hare-hare wadanda ke addabar babban birnin jihar ta Zamfara, wato Gusau.

Gwamnan a yunkurinsa na kakkabe 'yan bindiga da sauran bata gari daga jihar inda gwamnan ya kasance a farke tsawon dare yana bayar da umarnin yadda za a gudanar da samamen ga 'yan sandan musamman wadanda ke aikin bankado matsugunnan 'yan bindigan.

Wannan samamen an yi sa ne tsakanin karfe 10 na dare zuwa 5 na safe wanda ya yi sanadiyyar kama 'yan bindigar da dama, su da wadanda suke taimaka musu, wadanda suka hada harda wani ma'aikacin kashe gobara.

Majiyoyi sun bayyana cewa gwamnan ya yanke hukuncin ne sakamakon niyyar shi ta kawo karshen 'yan bindiga daga jihar. Ya tattaro bayanai ya kuma kasance mai bayar da umarni domin ya tabbatar da cewa ba wanda ya gujewa kamu a cikin wannan dare.

'Gwamnan ya shafe awoyi yana jagorantar yadda za a kaddamar da samamen har zuwa lokacin da aka kame shuwagabannin 'yan bindigar da ke damun Gusau, su da mataimakansu.' Kamar yadda majiyar ta shaida.

Wannan wani samame ne mai ban mamaki, domin gwamnan ya runka bayar da umarni ba tare da ya sanar da kowa a gidan gwamnati cewa ga inda ya samo bayanan sirri ba, ya tsara ya kuma kama wadanda ake zargin cikin nasara. Ya dage cewa duka wadanda ake zargin sai an kama su kafin safiya, haka kuma aka yi.

Bayan an kammala kamen na su, gwamnan ya duba wadanda aka kamo din, daga bisani kuma ya mika su zuwa ga kwamishinan 'yan sanda kafin a bayyana su a babbar cibiyar 'yan sandan Nijeriya ta jihar.

Kamar yadda gwamna Matawalle ya bayyana, wannan lokaci ne da jihar za ta dage wajen wanzar da zaman lafiya da kuma tsaron rayuka a jihar.

Wadanda ake zargin bayan kamasu an bayyana su a babbar cibiyar 'yan sanda ta jihar Zamfara wanda kakakin cibiyar 'yan sandan, kwamishinonin tsaro da kuma kwamishinan yada labarai suka jagoranta.

Bayan haka, bayanai sun nuna cewa Gwamna Matawalle tun lokacin da ya kasance ciyaman a majalisar kasa na kwamitin tsaro da leken asiri ya sha fada cewa shuwagabanni ya kamata su kasance a gaba-gaba wajen yakar rashin tsaro. Domin ya yi imanin cewa rushewar abinda aka tsara daga wadanda shugabanni ke amfani da su wajen warware matsalolin tsaro a kodayaushe na kara sa al'amurra su tabarbare.

Gwamnan ya sha bayyana cewa tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan kasa abu ne mai matukar muhimmanci, domin haka ya yanke hukuncin ya jagoranci wannan samame a matsayinsa na shugaban tsaro na jihar Zamfara domin kakkabe 'yan bindiga da sauran batagari.

'A yayin da wasu shuwagabanni suka fi mayar da hankali wajen zargin wasu a kan wannan al'amari mai matukar amfani, za mu cigaba da amfani lalama da kuma tsararawa domin fuskantar wannan matsala, a lokacin da komai daidaita, to sai mu duba mu gani su wa za mu yabawa da kuma su wa za mu zarga.'

'Za mu cigaba da fada duk wasu mutane ko kungiyoyi da  mataimakansu wadanda ke kawo hargitsi ga zaman lafiyar 'yanMatsalar tsaro a zamfara in ba a yabi matawalleba ba a sokeshi ba

A yau alkalaminmu zaiyi rubutune akan halin da jihar zamfara ta Shiga musamman a bangaren tsaro da Samar da zaman lafiya da kakaba mata wasu dokoki kowa yasan al’amarin ta’addanci ya zama ruwan dare a fadin tarayyar qasar mu baki daya.

Gwamnatoci a dukkan matakai suna iyakar qoqarin su na ganin an kawo qarshen lamarin wadda ya zuwa yanzu ya yi sanadiyyar rasa rayukan al’umma da dama da kuma janyo asarar dukiyar da dimbin Miliyoyin Nairori a ‘yan shekaraun nan. 

Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin yankin Arewa Maso Yammacin qasar nan da matsalar tsaro ta yi wa katutu, wananan ya kuma faru ne tun daga gwamnatocin da suka gabata, matakai da salon yadda suka fuskanci qoqarin warware matsalar tsaron a waccan lokacin ya taimaka wajen qara ruruwar wutan matsalar. Kuma hakan ya farune bisa rashin sani ko wani abu mai kama da hakan.

Akan haka dole a jinjina wa matakan da Gwamna jihar Zamfara, Alhaji Bello Mohammed Matawalle yake xauka don kawo qarshen matsalolin tsaro da ta addabi jihar ba kamar yadda wasu keta kokarin zai sun kawo mashi cikas a lamarin da fatan zasu hango kuskuren yin haka tare da don bashi had in kai shine mafitar jihar Zamfara.

In bamu mantaba a ‘yan shekarun nan kuma a daidai lokacin nan  wasu marasa kishi jihar ta Zamfara suna kai komo don kawo cikas akan kokarin Gwamna Matawallen amma ga dukkan alama Allah na tare dashi akan lamarin

Kar al'umma su manta da tunani Sake fasalin aikin jami’an tsaro da kuma tattaunawa kai tsaye da ‘yan ta’adda da nufin jawo hankalin su akan illar ayyuan ta’addancin da suke yi da kuma samar musu da wasu abubuwan kyautata raywa da zai taimaka musu nisantar ayyukan ta’addanci, wannann matakan kuma ya yi matuqar tasiri don ta wannan hanyar an samu nasarar ceto al’ummar jihar da ma wadanda ba ‘yan jihar bane da dama, lamari na baya bayan nan shi ne yadda aka ceto ‘yan mata masu yawan gaske yan asalin jihar Katsina. Gwamna Matawalle ya yi tsaye na ganin an tufatar dasu tare da kaisu don hada su da iyalan su ba tare da wata matsalama wannan abin jinjinane matuka.

Za a iya tilawar yadda matsalar tsaro ta ta’azzara a yankunan jihar Zamfara, tun fiye da shekara goma da suka wuce da rashin tsaro wanda ya yi sanadiyyar rasa dubban rayukan mutane da dukiyoyi na miliyoyin nairori sakamakon ayyukan ‘yan bindiga, a shekara ta farko lokacin zuwan gwamna Bello Mohammed ta yi qoqarin ceton rayukan mutane. An samu kwanciyar hankali inda mutane suka ci gaba da gudanar da rayuwarsu kamar yadda aka saba. Amma a cikin ‘yan kwanaki da makonni kaxan, tashin hankali ya sake dawowa a wasu yankuna da ke cikin jihar wadanda suka haxa da Kauran Namoda da Maru da kuma qaramar hukumar Talata-Mafara, inda aka yi asarar rayuka da dama sakamakon ayyukan ‘yan bindiga waxanda suka yi dirar miki a yankunan cikin dare.

Mafi yawancin shugabannin suna qoqari wajen kawo zaman lafiya, zaman lafiya ba ya samuwa haka nan dole sai an tashi tsaye kafin ake iya samun abin da ake buqata. Abin da ya fi qamari dai shi ne, yadda wasu suke son tashin hankali duk da qoqarin da gwamnatin take yi domin ta kare rayuwan mutane amm hakan bai samu ba. Da waxannan marasa son zaman lafiya, idan Matawalle yana san zaman lafiiya dole sai ya ba su abubuwan da suke buqata ciki har da sadaukar da rayukan mutane.

Duk da haka, Matawalle ba mutum ba ne da yake iya miqa kai cikin sauqi. Ya san wasu hanyoyi da zai iya bi domin ya samu nasarar cimma abubuwan da yake buqata. Wannan shi ne ya raba tsakanin shi da waxannan mutane. Ya samar da sabon matakai da zai tunkari matsalar rashin tsaro wanda ya bai wa jami’an tsaro umurnin a kai. A matsayinsa na shugaban tsaro na jihar, ya kasa sauke nauyin da ya rataya a kansa na kare rayuka da dokiyoyin mutanen jihar ba.

Gwamna Bello Mohammed ya xauki sabon matakai wanda ya gabatar wa shugaban qasa Muhammadu Buhari domin aiwatar da abubuwan da yake buqata. Xaya daga cikin su dai shi ne, saka na’urori wanda za a fara a kwanan nan. Shugaban rundunar sojojin sama, a kwakin baya ya ziyarci garin Gusau domin duba wannan aiki. Gwamna Matawalle ya yi amfani da wannan dama wajen yin gargadi da masu janyo tashin hankali da su sani gwamnati ta shirya yaqi da su. Ya sha alwashin ci gaba da yaqi da su domin kawo zaman lafiya ga mutanen Jihar Zamfara.

A kwanakin baya ne Matawalle ya yi ganawar sirri da masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro waxanda suka haxa da shuwagabannin tsaron da ke gudanar da aiki a jihar da dukkan shugabannin gargajiya da ke cikin jihar da malaman addini na jiha. A wajen wannan taro, gwamna Matawalle ya umurci dukkan shuwagabannin gargajiya da shugabannin qananan hukumomi su tsaya a yankunansu kar su kwana a ko’ina sai dai idan akwai wani mahimmin aiki.

“Saboda haka, na haramta wa duk wani mai riqe da sarauta da kuma shugaban qaramar hukuma kwana a wajen yankinsa, sai dai idan an samu wani yanayi na musamman. Za mu ci gaba da saka ido wajen kawo zaman lafiya a yankunanmu har na tsawon shekara xaya,” in ji gwamna Matawalle lokacin da yake sanar da su.

Amma duk da qoqarin da gwamna Bello Matawalle yake yi na kawo zaman lafiya a jihar, da yawa daga cikin maqiyan zaman lafiya a cikin jihar suna aiki kafaxa da kafaxa wajen rushe aniyarsa mai kyau wanda suke xaukan matakai da dama a kan haka.

cikin kwanakin nan ne aka samu nasarar ceto rayukan mutane 40 waxanda aka yi garkuwa da su ba tare da biyan kuxin fansa ba, musamman ma a Jihar Katsina wanda aka ceto ‘yan mata guda 26, wanda gwamna Bello Masari ya miqa su ga iyalansu.

Lalle ne duk iyayen da aka yi garkuwa da ‘ya’yansu sannan aka miqa su ga hannunsu, ko da maqi yansu ne sai sun nuna godiya ga wannan jan aiki musamman ma lokacin da aka miqa yaran cikin qoshin lafiya. Iyayen sun gudanar da waqoqin yabo da jinjinarsu ga gwamna Bello Mohanned, inda suka yi iqirarin cewa an samu nasarar dawo musu da ‘ya’yan su ne sakamakon shirin gwamna na zaman lafiya a cikin jihar.

Duk yanda lamura suka kasance, Gwamna Bello Mohammed bai tava neman yaban kowa ba na nuna shi ne ya samar da zaman lafiya a yankinsa. Idan da ya tava gudanar da hakan, to ba zai tava samun qoqarin ba a kan kawo zaman lafiya a cikin jihar wanda suka zo kafin shi sun gudanar da hakan. Gwamnatin Matawalle ba za ta shagwava ayyukan wani ba da gangan.

Allah shi kaxai zai yi hukunci bisa abin da mutane suke aikatawa. Allah yana bayan mai gaskiya. Yana bayan Matawalle wanda yake ta qoqarin kawo zaman lafiya ta kowani yanayi, duk da fuskantar ayyukan maqiya zaman lafiya, amma bai yi qasa a gwiwa ba wajen tsayar da zubar da jinin mutane a cikin jihar.

Dukda cewa wasu na ganin cewa duk matakan da matawalle yake dauka ba haka ya dace ba dole sai ra'ayin su ya dace abi wanda a gaskiya hakan ba adalci bane.

Ya zama dole a yaba wa matakan da Matawalle ke dauka don kawo qarshen matsalolin tsaro a jihar Zamfara, don kuwa matakan na haifar da xa mai ido.

Kumu wajibi mu bayar da goyan baya duk da halin yan Ubanci da wasu ke nuna mashi  bangarori da dama a halin yanzu amma da sannu duniya zata shaida hakan. 

Karshe muna rokon  Allah ya kawo zaman lafiya a fadin Nijeriya baki daya.

Kuma Allah ya haskakawa manyamu hanyar da ya dace abi. kasarmu, ba za mu kyale kowa ba.

No comments