Gwamna Tambuwal Da Mutawalle Sun Yi Ta'aziyyar Rasuwar Mahaifiyar Sarkin Kano


A jiya Litinin Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal da takwaransa na jihar Zamfara, Bello Muhammad Mutawalle suka kai ziyarar ta'aziyya ga Sarkin Kano bisa rasuwar mahaifiyarsa Hajiya Maryam Ado Bayero. Kamar yadda Muhammad Bello mai bai wa gwamnan Sakkwato shawara kan harkokin kafafen watsa labarai ya tabbatar a sanarwar da ya fitar. 

Gwamnonin biyu wanda suka samu rakiyar jiga-jigan jami'an gwamnati da abokansu daga jihohinsu har wala yau sun mika ta'aziyyarsu ga Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero wanda yake dan uwa ne ga Sarkin Kano. 

A cewar gwamna Tambuwal; "daga Allah muke kuma gare shi zamu koma. Muna wannan masarauta mai dimbin tarihi kuma gidanmu tare da abokina da sauran wakilai domin mika ta'aziyyarmu ga mai martaba Sarki da gwamnati da kuma al'ummar jihar Kano baki daya", ya bayyana. 

Ya ci gaba da cewa; "wannan babban rashi ne ga jihar da Nijeriya baki daya. Na kira na maka ta'aziyya lokacin da aka yi rasuwar. Ba mu zo nan a kan lokaci ba saboda rasuwar mutum biyu 'yan Sakkwato da ya faru", inji gwamnan inda ya yi kuma addu'ar rahama ga Marigayiyar. 

Sannan ya yi addu'ar samun zaman lafiya, walwala da kuma ci gaba ga kasar baki daya. 

A na shi bayanin, gwamna Mutawalle ya bayyana cewa; "kamar yadda takwarana kuma abokina ya ce mun zo nan ne domin yi maka ta'aziyya bisa wannan babban rashi. Ba mu zo akan lokaci ba saboda ta bangarena lokacin da aka yi rasuwar wadansu 'yan bindiga sun kai hari babban birnin jihar ta Gusau, inda suka kashe mutum 80", ya labarta. 

Gwamna Mutawalle ya ci gaba da cewa; "rashin nan ba naka bane kai kadai rashi ne gare mu baki daya," inji gwamnan, inda shima ya yi addu'a ga ruhin Marigayiyar tare da masarautar baki daya.

Da yake maida bayani, Sarkin Kano, ya mika godiyarsa ga gwamnonin bisa damar da suka samu har suka kawo masa ziyarar ta'aziyya duk da rashin lokaci isasshe da ba su da shi. "Ba ko tantama rasuwar mahaifiyarmu a bar kaunarmu rashi ne ga kowa", ya tabbatar. 

Haka zalika Sarkin ya bayyana cewa; "dukkanin rayuwarta ta rayu ne a nan cikin masarauta kafin daga bisani ta koma Gandun Albasa sa'annan ta sake dawowa cikin masarauta kafin rasuwarta. Sai muka dauka tasirinta bai wuce a tsakanin masarauta ba. Amma bayan rasuwarta sai mu ka ga ashe tasirin na ta ya zarce masarauta. Sai ga shi daga lungu da sako da kuma fitattun 'yan Nijeriya suna zuwa ta'aziyya", ya labarta, sannan ya yi addu'ar samun zaman lafiya ga kasar baki daya, tare da samun nasara a kan 'yan bindiga a arewa maso yammacin kasarnan, ya kuma yi addu'ar kawo karshen annobar cutar korona. 

A karshe ya sake jaddada godiyarsa ga gwamnonin bisa karfafa dadaddiyar alakar dake tsakanin Kano, Sakkwato da kuma Zamfara. 

Post a Comment

0 Comments