Daga Bala Musa
A jiya Laraba 6 ga watan Mayun 2021 ne, gwamnan Jljihar Neja ta fitar da sanarwar sauke Kwamishinan dake kula da ma'aikatan ayyukan jihar Injiniya Muhammaed Panti daga mukaminsa.
A kwanakin baya gwamnati ta sanya shi ya jagoranci binciken ma'aikatan Jihar wajen gano ma'aikatan boge.
Inda a yanzu kwamishinan ma'aikatar tsare-tsare Mamman Musa zai koma ma'aikatar ayyuka.
Sannan Alhaji Zakari Abubakar wanda shi ne kwamishinan kudi zai rika kulawa da ma'aikatar tsare-tsare ta Jihar Neja.
0 Comments