Gwamnatin Sojin Chadi Ta Ɗage Dokar Hana Fita

 


Gwamnatin sojin Chadi ta ɗage dokar hana fita da aka sanya bayan sanar da mutuwar shugaba Idriss Deby a ranar 20 ga Afrilu.

BBC Hausa ta labarto cewa; Jaridar da ke goyon bayan gwamnati ta Alwihda ta ce hukumomin sojin sun ce sun yake shawarar ɗage dokar ne bayan tabbatar da matakan da aka ɗauka.

Sanarwar da kakakin gwamnatin ya fiyar a cewar jaridar ɗage dokar zai fara aiki daga ranar Lahadi.


Post a Comment

0 Comments