A karon farko cikin shekara 11 bayan canjaras da Atlanta da ke ta biyu ta yi da Sassuolo, Inter Milan ta lashe gasar Seria A ta Italiya.
Inter ta bayar da maki 13 a saman tebur bayan nasarar da ta samu a ranar Asabar yayin da ya rage saura wasa hudu a kammala gasar.
Maki daya ne ya raba Inter da Juventus da ta lashe gasar a bara, sai dai a wannan karon Antonio Conte ya bai wa Juventus maki tara a shekara ta biyu da yake tafiyar da kungiyar.
Wannan ne kofin farko da kungiyar ta ci tun bayan lokacin da Mourinho ya tashe gasar Serie A da Champions League a 2010.
0 Comments