Kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta gargadi ga Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu akan cewa kada ya yi wasa da wuta bayan da Yahudawan Isra’ila suka raunata Falasdinawa kusan 200 a harin da Ć´an sandan Isra'ila suka kai musu a Kudus a ranar Juma'a.
Shugaban Hamas, Ismail Haniyeh ya ce, Falasdinawa za su ci gaba da ba da kariya ga unguwar Shaikh Jarrah da ke gabashin Kudus da aka mamaye, inda Isra’ilawa Ć´an kama wuri zauna ke ikirarin filayensu.
Isra’ila na ci gaba da zaluntar Falasdinawa din kan yiwuwar korar Falasdinawa daga yankin. Mafi yawan wadanda Isra’iliyawa suka raunata sun raunata su ne a harabar masallacin al-Aqsa lokacin da Ć´an sanda suka buÉ—e wuta da harsasai.
0 Comments