Jami'an Rundunar NSCDC 2, 300 Ne Za Su Bada Kariya A Wajen Bukukuwan Sallah A ZamfaraDaga Hussaini Yero, Gusau

Rundunar Jami'an farin kaya watau 'Nigeria Security and Defence Corp' ta tura jami'anta dubu biyu da dari uku domin bada kariya a wajen taron bukukuwan Sallah a fadin jihar Zamfara.

Kwamandan Rundunar na Jihar Zamfara, Aliyu Bature ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke tattaunawa da manema labarai a ofishinsa da ke Hedikwatar Rundunar a Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

Aliyu Bature ya bayyana cewa, domin ganin an yi bukukuwan Sallah lafiya a fadin jihar Zamfara, rundunarsa ta tura jami'anta dubu biyu da dari uku a lunguna da sako, Masallatai da Kasuwanni, da wajen wasannin gargajiya da cibiyoyin wasan yara, duk mun taro jami'an mu domin ganin an yi bukukuwan lafiya ba tare da matsala ba, inji Kwamandan.

Kwamandan Aliyu Bature ya kuma bada tabbacin kare rayukan al'umma a lokacin gudanar da bukukuwan Sallah da kuma dakile duk wani shirin da zai kawoma bukukuwan cikas a fadin Jihar.

Kuma Rundunar NSCDC ba za ta lamunci karya doka da aikata abubuwan da za su kawo rikici ko tashin hankali da wauta da abubuwan hawa ba a  wajan bukukuwan Sallah.

A karshe Kwamandan ya yi kira ga al'ummar Jihar Zamfara da su bi doka da Oda da kuma bamu rahoton abubuwan da al'umma ba su gamsu da su ba a wajen bukukuwan Sallah, dan daukar matakin gaggawa.

Post a Comment

0 Comments