Jami’ar Ahmadu Bello Zariya Ta Yi Rashin Babban LimamintaDaga Muhammad Farouk

Daya daga cikin Limaman Jami'ar ABU dake Zariya, Dr. Mustapha Isa Qasim ya rasu. Marigayin ya rasu ne bayan ya yi ta jinyar rashin lafiya a Asibitin koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello dake Shika. 

Bayanai sun nuna cewa Mustapha Isa Qasim ya dauki shekara da shekaru ya na koyar da addini. Sai dai a daren Laraba, 12 ga watan Mayu, Liman Mustapha Isa Qasim ya rasu ya na da shekara 60 a duniya. 

MADOGARA ta labarto cewa ‘yan'uwan Marigayin sun tabbatar mana da rasuwar Malamin na Boko da addinin Musulunci a asibitin koyon aiki na ABUTH da ke Shika. 

Kafin rasuwarsa, Mustapha Isa Qasim, mataimakin Farfesa ne a sashen koyar da addinin musulunci a jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria. 

Marigayin ya shafe shekaru kimanin 30 a ABU Zaria, ya taba rike makarantar koyon musulunci da ilmin shari’a da ke garin Misau, jihar Bauchi 

Bayan Limancin da Malamin yake yi a wadannan masallatai, ya dauki shekaru kusan 40 ya na koyar da addinin musulunci a garin Zariya, jihar Kaduna 

An jana’izarsa a yau 30 ga watan Ramadan da karfe 1:30 na rana a jami'ar. 

Liman Mustapha Isa Qasim ya rasu ya bar mata uku, ‘ya ‘ya 17, da jikoki masu yawa. 


A shekarar bara ne daya daga cikin limaman farko na fitacciyar jami’ar nan ta Ahmadu Bello da ke Zariya, Imam Abubakar Musa ya rasu. A ranar Lahadi, 19 ga Watan Junairun 2020, Limamin ya rasu ya na da shekaru kusan 110. Imam ya rasu, ya bar Mata biyu da ‘Ya ‘ya 46 da kuma jikoki rututu. 

Post a Comment

0 Comments