Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jam'iyyar APC Ta Yi Zaben Maye Gurbi A Karamar Hukumar Sabon Gari Ta Jihar Kaduna

     Daga Hagu; Hon. Shagali sai Hon. Musa Daga Fatima Idris Zariya A ranar Asabar ne 22 ga watan Mayu na  shekarar 2021, jam...

     Daga Hagu; Hon. Shagali sai Hon. Musa


Daga Fatima Idris Zariya

A ranar Asabar ne 22 ga watan Mayu na  shekarar 2021, jam'iyyar APC ta karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna ta gudanar da zaben maye gurbi na dan majalisa da aka sauke sakamakon rashin halartar shi majalisa na tsawon wasu lokuta da da ake zarginsa. Honorabul Aminu Shagali, tsohon shugaban majalisar wakilai na jihar Kaduna karkashin gwamnatin Malam Nasiru El-Rufai shine aka tumbuke bisa zarginsa da rashin halartar majalisar na wasu lokuta.

Rashin halattar nasa ya haddasa bayyana shi a matsayin korarren dan majalisa. Wannan dalilin ne ya sa jam'iyyar APC ta bayar da ranar 22 ga watan 5 don gudanar da zaben maye gurbi a shiyyar da dan takarar ya fito, wato karamar hukumar Sabon Gari.

Wakilin MADOGARA ya halarci wurin zaben, kuma ya shaida yadda zaben ya kaya.

Shuwagabannin jam'iyya da masu fada a ji da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC ne suka yi dandazo a makarantar gwamnati da ake kira Hanwa Primary School don gudanar da zaben maye gurbin. Malaman zaben sun shelantawa masu kada kuri'un cewa Honorabul Musa A. Musa ne tilo ya sayi fom na tsayawa takara a jam'iyyar APC amma duk da haka za a gudanar da zabe kamar yadda doka ta tanada.

Bisa haka, jama'a suka kadawa Honorabul Musa A. Musa kuri'unsu don maye gurbin wancan dan majalisa da aka sauke.

Shuwagabannin APC da wakilan INEC suka sa ido wajen gudanar da zaben inda aka tantance akalla kuri'u wajen 8000, kuma an samu damar kada kuri'u 6,805 wanda hakan ya ba shi Honorabul Musa A. Musa damar zama cikakken dan takarar kujerar majalisa mai wakiltar Sabon Gari a karamar hukumar Sabon Gari.

Bayan kammala zabe, wakilinmu ya zanta da daya daga cikin malaman zabe, Malam Nura Audi Usman, daya daga cikin kwamitin da suka lura da zaben, ya bayyana cewa babu wata matsala da suka samu yayin gudanar da zabe, Musa A. Musa ne suka sani a zaben maye gurbi na kujerar dan majalisa kuma an yi lafiya an tashi lafiya.

Shima Honorabul Musa A. Musa A yayin da ya ke zantawa da manema labarai, ya nuna jin dadi da amincewa da abin da ya gudana yayin gudanar da zaben, karshe ya nuna jin dadinsa game da zabensa da jama'a suka yi don cike gurbin kujerar majalisar jiha a wannan lokaci, ya roki Allah Ya maida kowa gida lafiya.

No comments