Javad Zarif Ya Nemi Afuwar Iyalan Qassem Soleimani

 


Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya nemi afuwa ga iyalan tsohon kwamandan kasar marigayi Qassem Soleimani kamar yadda BBC ta labarto.

Hakan ya biyo bayan wani sauti da aka nada, da aka ji ministan na sukar Qasem Soleimani kan yin katsalandan a harkokin diflomasiyyar Iran.

A bara ne Amurka ta kashe Mr Soleimani a wani hari ta sama lokacin da yaje Iraki.

Kwamandan da ke runduna ta musamman a kasar na daya daga cikin mutane masu muhimmanci a Iran.

Post a Comment

0 Comments