Ka Kawo Karshen Matsalar Tsaro Ko A Tsige Ka -Sakon Kungiyar Dattawan Arewa Ga Buhari


Mai magana da yawun kungiyar Dattawan 'yan Arewacin Najeriya, Dr Hakeem Baba-Ahmed ya bukaci Majalisar dokoki da ta tsige shugaban kasa Muhammadu Buhari idan ya kasa sauke nauyin da ya rataya akan sa na kare lafiya da dukiyoyin jama’a.


Baba-Ahmed ya ce Najeriya na matukar neman shugabanci a wannan lokaci saboda haka ana bukatar aiki a zahiri maimakon magana ko kuma yiwa jama’a alkawuran da ba’a cikawa.

Mai magana da yawun kungiyar Dattawan ya ce 'yan Majalisu na da hurumin nazarin halin da kasa ke ciki da kuma dubi akan abinda gwamnati tace tana yi da kuma tanade-tanaden da kundin tsarin mulki yayi domin daukar mataki akai.

Baba-Ahmed ya ce muddin Buhari ya gaza sauke nauyin da ke kan sa, shi bai ga dalilin da zai sa Majalisa ba za ta dauki mataki akan sa ba.

Tsohon babban Sakataren gwamnatin Najeriyar ya yi tambaya inda ya ke cewa a shekaru biyu da suka gabata babu wani abinda shugaban kasar ya yi da zai karfafa gwiwar jama’a wajen kare rayukan su, saboda haka babu dalilin da zai sa ba za a tsige shugaban ba idan ya gaza.

Baba-Ahmed ya ce abin takaici Najeriya ba ta da Majalisar da ke da kishin kasa da kuma halin da ake ciki ba, sai dai mai goyan bayan jam’iyyar ‘yayan ta suka fito.

Maslaha ta biyu ita ce 'yan kasa su dauki mataki na kashin kan su, ko kuma na 3 wadanda nauyin shugabanci ya rataya akan su su aje mukaman su saboda gazawa.

Post a Comment

0 Comments