Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Nijeriya ta ce ƙarin mutum 30 ne suka kamu da cutar korona cikin awa 24 da suka wuce a ƙasar. Cikin ...
Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Nijeriya ta ce ƙarin mutum 30 ne suka kamu da cutar korona cikin awa 24 da suka wuce a ƙasar.
Cikin rahoto na kullum da take wallafawa, NCDC ta ce sabbin kamuwar sun fito ne daga jihohi guda uku.
Jihohin su ne Legas mai mutum 26, da Rivers mai uku, sai kuma Kwara mai mutum ɗaya.
Ya zuwa yanzu, cutar korona ta kama mutum 166,315 jumilla a Najeriya, kazalika ta kashe mutum 2,071, sai kuma 156,558 da aka sallama bayan sun warke.
No comments