![]() |
Shugaban hukumar zabe na NIjeriya INEC Farfesa Mahmud Yakubu. |
Hukumar zabe mai zaman kanta ta
Nijeriya ta samu wani gagarumin dama a daidai lokacin da Kotun kolin Nijeriya
ta yanke hukuncin cewar hukumar na da hurumin soke wasu jam’iyyun siyasar kasar
da suka gaza wajen taka rawar lashe wasu kujerun majalisu ko na gwamnoni ko kuma
shugaban kasa.
Wannan ya biyo bayan karar da
Jam’iyyar NUP ta shigar inda ta ke kalubalantar hukumar zaben kan matakin da ta
dauka na janye lasisin ta da na wasu jam’iyyun kasar 74.
Mai shari’a Chima Nweze ya ce
matakin da hukumar zaben ta dauka ya yi daidai da dokar kasa da kuma dokar zabe
da ake amfani da ita a kasar.
Kafin wannan hukunci a jiya babban
kotun Abuja da ta daukaka kara duk sun amince da matsayin hukumar zaben na soke
lasisin Jam’iyyu 74 saboda gaza lashe koda kujerar majalisa guda.
0 Comments