Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Advertisement

Pages

Labarai:

latest

Advertisement

Ku Yi Hakuri Ku Saki Daliban Jami'ar Greenfield -Rokon Shugaba Buhari Ga 'Yan Bindiga

Daga Muhammad Farouk Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan bindigar da ke ci gaba da garkuwa da daliban Jami'ar Gr...


Daga Muhammad Farouk

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki 'yan bindigar da ke ci gaba da garkuwa da daliban Jami'ar Greenfield da su yi wa Allah su kuma yi hakuri su saki daliban da dukkanin sauran 'yan kasa da ake ci gaba da garkuwa da su. 

Shugaban ya bayyana hakan ne a jiya Laraba a shafinsa na Facebook a cikin sakon murnar da ya aika kan sakin daliban Makarantar koyon aikin gona da Gandun Daji dake Afaka ta jihar Kaduna. Inda shugaban kasar ya ce; "ina sake rokon da a saki daliban Jami'ar Greenfield da dukkanin sauran 'yan kasa da ake ci gaba da garkuwa da su. Za mu tabbatar da kowanne dan Nijeriya ya rayu a kasar da zai iya zuwa duk inda yaso ba tare da tsoron garkuwa da shi ko kai masa hari ba", inji shi.  

Shugaban a bayaninsa har wala yau ya ce; "ina murnar sakin dalibai 27 na Makarantar koyon aikin gona da Gandun Daji ta gwamnatin Tarayya dake Afaka, ina taya abokansu da iyalinsu da al'umma da gwamnatin Kaduna murna. Na ji dadi an sake su", ya tabbatar.  

Shugaban ya mika godiyarsa ga duk wanda ya taimaka aka samu nasarar 'yanto daliban musamman hukumomin tsaro, ma'aikatar muhalli da kuma gwamnatin Kaduna. "Muna mika godiya ga 'yan Nijeriya da addu'o'insu". 

Shugaba Buhari ya nemi da hukumomin tsaro su wayar da kan al'umma kan tsaro da samun hadin kansu. Ya nemi kuma dukkanin al'umma a hada hannu wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali tare da nisantar siyasantar da tsaron kasar. Inda ya ce abin Allah-wadai yadda wadansu 'yan siyasa ke siyasa da tsaron Nijeriya. 

No comments