Kungiyar Masu Motoci Ta RTEAN Ta Kaddamar Da Shirin Inshora Ga Matafiya


Daga Bello Hamza 

Kungiyar masu sufurin motoci na RTEAN ta samu nasara kaddamar da shirin samar da inshora ga matafiya da aka yi wa lakabi da ‘Travelers Accident Insurance Scheme (TAIS)’ ana kuma sa ran miliyoyin ‘yan Nijeriya ne za su amfana wadanda ke tafiye tafiye daga tashoshin mota a kasar nan, musamman in har suka samu hatsarin da ake bukatar agajin gaggawa, wannan kuma wani kokari e na kungiyar don tallafa wa al’umma tare da kuma karfafa bangaren sufuri na kasar nan gaba aya.

Shugaban kungiyar ta RTEAN, Alhaji Musa Muhammed Maitakobi ya bayyana haka a takardar sanarwa da ya raba wa mana labarai a garin Abuja, ya kuma kara da cewa,

Tafiye-tafiye da mota nada mtukar mahimamnci, musamman ganin al’umma da dama sun dogara da shi wajen zirga-zirga da kuma neman abin rufa wa kansu asiri  haka kuma shirin zai samar wa da al’umma da dama aikin yi don kuwa miliyoyin al’umma suka dogara da harkar sufuri a kasar nan. Muna kuma goyon bayan gwmanatin tarayya a kokarin ta na samar wa al’umma da ayyukan yi a fadin tarayyar kasar nan da kuma bukatar samar da motoci na zamani masu amfani na wutar lantarki don rage gurbatar yanayi da kuma dumamar yanayi.

Ya kuma kara da cewa, “Aikinmu shi ne inganta sana’ar tuki ta zama ana mahimantar da motar da kuma samar da direbobi masu bin dokoki da kuma ka’dojin hanya gaba daya.

Shugaban kungiyar ya kuma yi amfani da damar wajen mika godiyar kungiyar ga sakataren gwamnatin tarayya da kuma ministan sufuri a kan yadda suke ba kungiyar goyon baya a dukkan lokutta.

Tunda farko, a jawabinsa mataimakin shugaban kwamitin kula da harkokin sufuri na majalisar dattawa, Sanata Nicholas Tofowomo ya bukaci gwamnati a dukkan matakai su taimaka wajen karfafa harkar sufuri don a samu nasara da ya kamata, ta yadda al’ummar kasa za su amfana da shirin da ake bulo da shi don inganta harkar sufuri a Nijeriya.

Sanata Nicholas Tofowomo ya kuma tabbatar wa al’umma cewa, majalisar dattawa za ta samar da dokar samar da tsarin inshora na matafiya don dukkan mas ruwa da tsaki su amfana, ya kuma yaba wa shugaban kungiyuar RTEAN akan yada yake samar da cigaba da za su amfani al’umma Nijeriya.

Post a Comment

0 Comments