Tafiyar Kwankwasiyya a Kano na
fuskantar mummunar rikicin cikin gida tsakanin mambobinta a cikin Yan makonnin da suka gabata.
Wannan na zuwa ne bayan daya daga
cikin masu ruwa da tsaki da shugabanninta a Kano suka raba kayan abinci na
miliyoyin nairori a matsayin wani bangare na tallafin Azumin watan Ramadan ga
mambobinta.
An ga wani na hannun daman Kwankwaso Sanusi
Surajo a wani bidiyo da ya yadu a yanar gizo,inda yake zargin Dakta Yunusa
Adamu Dangwani da kokarin wargaza tafiyar saboda burinsa na takarar gwamna.
Sanusi Surajo ya sake jaddada cewa
ba za su kara yarda da kowane dan takara ba in ba Abba Kabir Yusuf ba, yana
kiran Dangwani ya ajiye da burinsa ko kuma ya fice daga tafiyar ta
Kwankwasiyya.
“Ko Kwankwaso ba zai iya canza mana Abba ba,
idan ba za ku goyi bayan Abba ba gara ku fice daga Wannan tafiyar ko ku sauya
sheka daga jam’iyyar.
Abba ya sami goyon bayan mutane, mutane sun
yarda da shi, ba za mu iya canza shi ba, amma mun san cewa yana yin wadannan
yunkurin ne domin yi wa Kwankwaso zagon kasa amma Allah Yana ganinsu kuma ba za
su yi nasara ba.
Duk da cewa ya ki ambatar suna, amma sakon
nasa ya bayyana karara cewa yana bayanine akan Dakta Yunusa Dangwani, tsohon
Shugaban Ma’aikatan Kwankwaso kuma Kwamishinan albarkatun ruwa lokacin da
kwankwaso yake gwamna a wa’adi na biyu.
Dangwani ya kasance a cikin zargi ne
tun lokacin da ya raba kayan azumin Ramadan ga mambobin jam’iyyar.
Tun daga lokacin ya ji ‘ya’ya da
masu ruwa da tsakin Kwankwasiyya suna goyon bayansa dangane da kiransa ya fito
takarada takarar gwamnan Kano a Shekara ta 2023
Tun fitowar sa Matsayin dan takarar kujerar
gwamnan jihar a karkashin jam’iyyar PDP, Abba k Yusuf yake ta jin kansa, baya
girmama kowa kuma yana amfani da wasu mambobin wajen cin zarafin wasu masu ruwa
da tsaki a kokarin da yake na musguna musu.
Wannan shi ne dalilin da ya sa bama son Abba,
ko da kuwa ya yi nasara, zai ajiye shugabanninmu a gefe, ba Zai yi aiki tare
dasu ba. Wani memban kungiyar da ya Nemi
a sakaye sunansa ya fada.
A cewar wasu, ba Yunusa Adamu
Dangwani ne kawai Cikinmai ruwa da tsaki a Kwankwasiyya da basa jituwa da Abba
Kabir Yusuf ba,yawancin shugabannin kungiyar suna goyon bayan yunkurin da
Dangwanin keyi.
A wani bangaren Kuma Wasu masu ruwa
da tsaki sun nuna rashin amincewarsu da shawarar da Kwankwaso ya yanke na kawo
Mohammed Yusuf Jamo a matsayin mataimakin shugaban PDP na shiyyar Arewa maso
Yamma da Mustapha Alkassim Dan Hajiya a matsayin Ex-officio.
A cewar wani na hannun daman
Kwankwaso wanda ya nemi a sakaye sunansa yace, Kwankwaso kai tsaye ya kawo
mutanen biyu ba tare da tuntubar Masu Ruwa da tsakin a tawagarsa ta
Kwankwasiyya ba.
Wata Majiya ta ce Kwankwaso a shirye
yake ya fice daga PDP idan har ya gaza tabbatar da kujerar Mataimakin Shugaban
Jam’iyyar na shiyya ga mutumin nasa.
Lokacin da Politics DIGEST ta tuntubi daya
daga cikin makusantan tsohon gwamnan ko a shirye suke su bi sa tare da ficewa
daga jam’iyyar, sai ya ce A’a kuma da yawa daga cikin mutanen sa ba za su bi
shi ba idan ya yanke wannan shawarar.
Daga cikin ‘yan Kwankwasiyya masu
adawa da takarar Abba Kabir Yusuf sun hada da Aliyu Sani Madaki, Yusuf Bello
Dambatta, Barr. Maliki Kuliya, Farfesa
Umar Farouk Jibril, Danburan Abubakar Nuhu, Zainab Audu Bako, Lawan Sale Gaya,
Garba Ibrahim Diso da sauransu.
Gabanin zaben 2019, makusantan tsohon Sanatan
da suka watsar da shi kamar Aminu Dabo, Bala Gwagwarwa, Muaz Magaji da Idris
Dambazau sun fice daga tafiyar saboda zabar Abba Kabir Yusuf Matsayin Dantakar
gwamnan Kano.
0 Comments