Lambar NIN Za Ta Magance Wasu Matsalolin Tsaro, Inji Shugaba Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sabon shirin haɗa lambar ɗan ƙasa ta National Identification Number (NIN) da lambar waya zai tallafa wajen gano miyagu a ƙasar kamar yadda Bbc Hausa ta labarto. 

Saboda haka ne ya shawarci 'yan Najeriya da su shiga a dama da su a shirin, wanda ya ce zai taimaka wajen samar da bayanai na intanet da za su taiamaka wa tsaron ƙasa.

Shugaban na magana ne yayin ƙaddamar da shirin Revised National Identity Policy wato sabon tsarin samar da lambar ɗan ƙasa a fadarsa da ke Abuja.

"Lambar NIN za ta gyara wasu daga cikin matsalolinmu na tsaro," in ji shi. "Cikin sauƙi za mu san kowane mutum a Najeriya sannan ta taimaka wajen haɓaka tsaro.

"Lambar wata shaida ce ta ƙasa, ya kamata 'yan Najeriya da kuma waɗanda ke da izinin zama su same ta. Da ita mutum zai samu ayyukan gwamnati sannan ta taimaka mana wajen aiwatar da nagartattun ayyuka cikin ƙwarewa."

Yayin taron ne Ministan Sadarwa Isa Ali Pantami ya gabatar wa da Buhari da sauran manyan jami'an gwamnati sabon katin shaidarsu na ɗan ƙasa mai ɗauke da lambar ta NIN.

Ranar Litinin ne ministan ya ƙara wa'adin haɗa NIN da layukan wayar salula zuwa 30 ga watan Yuni.

Alƙaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa mutum miliyan 54 ne suka haɗa lambar tasu da layin waya, abin da ke nufin layin waya kimanin miliyan 200 na da rajista da lambar NIN, a cewar hukumar NCC.

Post a Comment

0 Comments