Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Luguden Wuta Da Isra'ila Ta Yi A Gaza Ya Kashe Mutum 120 Da Jikkata 830

Daga Muhammad Farouk Haramtacciyar Gwamnatin Isra'ila da suka share wuri suka zauna na ci gaba da luguden wuta ta sama da ka...


Daga Muhammad Farouk

Haramtacciyar Gwamnatin Isra'ila da suka share wuri suka zauna na ci gaba da luguden wuta ta sama da kasa a kan Gaza ta kasar Falasdinu inda suka kashe akalla mutum 120 ciki harda kananan yara da mata.

Rundunar sojin Haramtacciyar Gwamnatin Isra'ila ta ce hare-haren da ta kaddamar cikin dare sun hada da na jiragen yaki da tankuna a kan wata hanyar bututun karkashin kasa da Hamas ta gina a yankunan fararen hula, sai dai ta ce a wannan karon ba ta samu damar ankarar da fararen hula kamar yadda ta yi gabanin hare-haren da ta kaddamar a hasumiyar Gaza a makon da ya gabata ba.

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ruwaito cewa  gidaje da dama a yankunan Gaza da ke da yawan jama’a ne suka salwanta, a yayin da ministan Lafiyar Gaza ya ce yanzu haka ya lakume rayukan Falasdinawa 119 ciki har da yara 31, ya kuma raunata 830.

Kafafen watsa labaran yammaci sun ce wata mata, Bayahudiya, wacce ta zarce shekaru 80 da haihuwa ta rasu a cikin daren Alhamis sakamakon raunukan da ta samu a yayin da take neman mafaka daga rokokin da ake harbawa, abin da ya kawo adadin mamata a bangaren Isra’ila guda 9. 

Ya zuwa hada rahoton nan, sama da rokoki dubu 1 da 800 ne mayakan Hamas suka harba a Haramtacciyar kasar ta Isra’ila, akasari a biranen kudancin kasar, wanda rokokin suka dira har da Tel Aviv da Jerusalem inda Yahudawan Sahyoniya suke wanda kuma ya yi musu asara ba karami ba, inda kafafen watsa labarai na yammaci ke boye irin hasarar da Haramtacciyar Gwamnatin Isra'ila ta yi. 

No comments