Malami Mafi Karancin Shekaru Da Ke Tafsirin Alkur'ani A Zariya


A yau Litinin ya zo daidai da 28 ga watan Ramadana inda Sheikh Zakeek MS Ali wanda aka fi sani da Young Sheikh yake rufe Tafsirin Alkur'ani mai girma na wannan shekarar.

Rahotanni sun nuna cewa yana gabatar da Tafsirin ne a gidan 'Maulana Sheikh Aliyu Mai Yasin Zariya', kamar yadda shafin Kasar Zazzau Jiya Da Yau ya tabbatar. 

Sheikh Zakeek MS Ali ya kasance da ne a ga Garkuwan Makarantar Zazzau, kuma shi ne Malami mafi karancin shekaru da yake Tafsirin Alqur'ani mai girma a fadin kasarnan.

Ga wasu hotuna daga wurin Tafsirin;

Post a Comment

0 Comments