Malami Ya Ce An Gano Manyan Mutanen Dake Daukar Nauyin Ta’addanci A Nijeriya


Ministan shari’ar NIjeriya, Abubakar Malami ya ce binciken da suka gudanar ya nuna musu wasu fitattun 'yan NIjeriya da kuma 'yan kasuwar da ke daukar nauyin ayyukan ta’addanci a cikin kasar.

Ministan ya ce tuni aka fara shirin gurfanar da wadannan mutane a gaban kotu domin fuskantar shari’a akan rawar da su ke takawa wajen haifar da tashin hankali sakamakon binciken da gwamnati ta gudanar a Daular Larabawa dangane da masu daukar nauyin bai wa boko haram kudade.

Wannan matsayi na gwamnati na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fuskantar karuwar hare-haren ayyukan ta’addanci na Boko haram a yankin arewa maso gabas da kuma wasu hare-haren na daban a wasu yankuna musamman arewa maso yamma.

Malami ya ce gwamnati ta dauki dogon lokaci ta na gudanar da bincike akan wannan lamarin da ya shafi ayyukan ta’addanci bayan da kotu a Daular Larabawa ta daure wasu 'yan Nijeriyar guda shida.

Ministan ya ce binciken da suka dauki dogon lokaci su na yi ya nuna musu wasu mutane da hukumomi da ke da hannu wajen jefa kasar cikin tashin hankali.

Malami ya ce suna da kwararan shaidu da ke nuna musu irin wadannan mutanen da ke daukar nauyin baiwa 'yan ta’adda kudade kuma yanzu kotu ce za ta tabbatar da wannan zargi.

Post a Comment

0 Comments