Man City Ta Kai Wasan Karshe Na Gasar Zakarun Turai A Karon Farko A Tarihinta

 


Manchester City ta lallasa Paris St Germain da ci 2-0 a wasan daf da karshe zagaye na biyu na gasar neman cin kofin zakarun Turai, kuma ta haye matakin wasan karshe wato final a karon farko.

Riyad Mahrez ya ciwa City kwalleyen biyu da ya bata wannan gagarumin nasara a fafatawar da sukayi daren jiya a Ethihad.

A wasan farko da suka kara a Faransa a makon jiya City’n ce ta yi nasara da ci 2-1, idan aka hada da na jiya, ta samu jummular kwalleye 4-1 kenan gida da waje.

PSG wadda tayi wasan na jiya ba tare da gwarzon dan wasanta Mpampe da yaci kwallo 10 a gasar na zakarun ba, tayi ta kokari amma batayi nasara ba, hasalima sai da ta karasa wasan da ‘yan kwallo 10, bayan da aka bai wa Angel Di Maria jan kati.

Laraban nan Chelsea za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan daf da karshe zagaye na biyu na gasar Champions League da za su fafata a Stamford Bridge.

A wasan farko da suka kara makon jiya a gidan Madrid kungiyoyin biyu sun tashi  1-1, wato Chelsea nada dama kenan.

 


Post a Comment

0 Comments