Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Masu Bautan Gumaka A Indiya Sun Fara Jefar Da Danyen Mangwaro Su Huta Da Kuda

Shiawaves ta ruwaito cewa Jama'a da dama a qasar Indiya sun zubar da gumakan da suke bautawa a tituna a yayin da adadin wada...


Shiawaves ta ruwaito cewa Jama'a da dama a qasar Indiya sun zubar da gumakan da suke bautawa a tituna a yayin da adadin wadanda ke kamuwa da cutar korona ke karuwa a kasar sannan cutar na cigaba da kisa.

Wasu ‘yan qasar sun nuna bacin ransu ga gumakan da suke bautawa tare da yi musu hidima amma sun gaza kare su daga annobar ta korona.

Sun rika yin addu'o'i ga gumakan da suke bautawa suna masu imanin za su kare su daga kwayar cutar amma daga karshe sun gano cewa abin da suke nema bai samu ba sai suka yi watsi da su.

Adadin mutanen da ke kamuwa da cutar korona a kowanne rana a Indiya ya kai 3,3780 sannan adadin wadanda cutar ta halaka ya dara miliyan 20.

Asibitoci a kasar na Indiya sun cika makil hakan kuma ya janyo karancin magunguna, iskar oxyegen da gado domin kwantar da marasa lafiya.

Rashin samun gado a asibitin da karancin magungunan ya janyo wasu masu jinyar suna galabaita sosai ko rasa rayukansu ba tare da sun samu taimakon da suke bukata ba.

No comments