Mun Gano Sabon Makircin Da Aka Kulla Da Sunanmu –Mabiya Harkar Musulunci Sun Fallasa

 


-Kaddamar Da Ta’addanci Ba Ya Daga Cikin Manufofinmu

By Muhammad Farouk

Mabiya Harkar Musulunci a Nijeriya da aka fi sani da ‘yan shi’a a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky sun bayyana cewa sun gano wani sabon makirci da aka kulla da sunan su, kuma sun barranta da hakan. Mabiya Harkar sun bayyana hakan ne a sanarwar manema labarai da suka fitar wanda shugaban dandalin yada labarai na Harkar, Ibrahim Musa ya sanyawa hannu kuma MADOGARA ta samu kwafin takardar.

Sanarwar ta nuna cewa: “gwamnatin Buhari a kokarinta na murkushe Harkar Musulunci a Nijeriya wanda ta fara tun lokacin kisan kiyashin Zariya da sojojin Nijeriya suka yi a watan Disambar 2015, gwamnatin ta ci gaba da wannan aikin. A wannan karon, gwamnatin tana son yin amfani da wani makirci wajen kaddamar da wani aiki domin batawa Harkar Musulunci suna”, inji sanarwar.

Bayanin ya ci gaba da cewa: “ya zama wajibi mu cire shakkun cewa amfani da hanyar ta’addanci ba ya daga cikin manufarmu, kuma ba zai taba zama ba, kamar yadda yake a bayyane na yadda muke gudanar da harkokinmu cikin lumana duk da irin musguna da gwamnatin ke yi mana na tsawon shekaru biyar”, suka tabbatar.

Harkar Musuluncin sun ci gaba da cewa; “wannan matakin namu da muke dauka ba zai sauya ba. A don haka wannan manufar gwamnati ce kawai da ta kulla makirci ta hanyar rubutu da sunan wata kungiya da ba a santa ba da suke kokarin danganta ta da Harkar Musulunci a Nijeriya da suke fafutikar ganin an saki Shaikh Ibraheem Zakzaky daga daurin zalunci da ake masa”, ya nusasshe.

Ya kuma labarta cewa; “wannan kungiyar da ba a santa ba an kirkireta ne domin amfani da ita a muzaharar lumana ta Kudus na shekara-shekara da muka saba yi domin ta haifar da abu mara kyau”, ya lurantar.

Har wala yau Harkar Musuluncin ta ce duba da wannan suna mai sake jaddada matsayar jagoransu Shaikh Ibraheem Zakzaky, wanda suka ce tsawon shekara fiye da shekara arba’in da ya kwashe a matsayin jagoran Harkar Musulunci bai taba amfani da ta’addanci a matsayin wata hanyar cimma manufar Harkar Musulunci ba. “ya yi imani da amfani da hanyoyin lumana a ayyukan addininsa. Muzahara da gangamin ranar Kudus zai zo ne a ranar Juma’a 7 ga watan Mayun 2021, kuma taro ne na duniya da ake gudanar da shi a birane. Kuma bai taba zama ranar da ake amfani da shi wajen tashin hankali ko rikici ba domin wayar da kan al’umma dangane da zalunci da danniya da wariyar da Yahudawan Haramtacciyar kasar Isra’ila ke nunawa al’ummar Falastinu”, sanarwar ta tabbatar.

“ka da mu manta wannan ba shi ne karon farko da gwamnati ta yi yunkurin amfani da makirci wajen alakanta Harkar Musulunci da ta’addanci ba. Bayan kisan kiyashin Zariya, rundunar soji ta biya Malamai sun rika wa’azi suna cewa; “Harkar Musulunci ta fi Boko Haram hadari” domin tabbatar da kisan kiyashin da suka yi. Gami da karawa, al’umma ta ki amincewa da wannan farfagandar wanda hakan ya sanya hatta Amurka ta ce Shaikh Zakzaky fursunan siyasa ne kuma Harkar Musulunci na fuskantar zalunci daga gwamnatin Buhari. A don haka ba za ku alakanta mu da ta’addancin da jami’an gwamnati suke son kaddamarwa da sunanmu ba”, ya jaddada.

Ya kuma kara da cewa; “suna son nade tabarmar kunya da hauka ne saboda sun kasa bizne ta’addancin da suka yi, kuma sun gaza nasarar kulla ma Harkar makirci a kotuna mabambanta”, ya lurantar.

A karshe sun jaddada bukatarsu, inda suka nemi gwamnati ta saki jagoransu Shaikh Ibraheem Zakzaky da matarsa  wanda ake ci gaba da rike su tun Disambar 2015; “daga karshe, sama da shekara biyar gwamnati ta ki ta saurari muryoyin da suka dace wajen sakin jagoranmu Shaikh Zakzaky da matarsa da sauran wadanda suke tsare tun watan Disambar 2015. A don haka muna kira ga dukkanin wani dan Nijeriya mai hankali da sauran al’ummar duniya da su fito su nemi ganin ‘yancin jagoranmu”, ya jaddada.

 

Post a Comment

0 Comments