Mutanen Gari Sun Cafke 'Yan Bindiga Bayan Sun Lakada Musu Duka A KanoWadansu 'yan bindiga sun shiga hannu bayan da suka shiga Unguwar Yamadawa dake Dorayi Babba a karamar Hukumar Gwale dake jihar Kano, inda al'ummar unguwar suka yi Kukan kura suka kama su bayan da suka yi yunkurin yi wa wani mutum fashi da misalin karfe 11 na daren ranar Laraba. 

Gidan Rediyon Freedom Kano ya labarto cewa wadansu ganau sun shaida masa cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Laraba, inda 'yan fashin guda biyu suka fito da bindiga domin yiwa wani tsoho fashi a yayin da yake kokarin shiga gida. 

Lamarin da ya ja hankalin al'ummar unguwar dake kusa inda suka yi azama suka rarumi 'yan bindigar da suka yi harbe-harbe suka kuma yi yunkurin guduwa a daidaita sahu. 

Mutanen Unguwar sun musu duka tare da cafke su inda suka mikawa 'yan sandan yankin su. 

A cewar wani ganau ya ce 'yan sanda sun kai 'yan bindigar da ake zargi asibiti saboda an yi musu jina-jina a yayin da aka kama su.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar a yau Alhamis. 

Sanarwar ta ce an samu bindiga da wuka daga hannun 'yan bindigar a yayin da suke kokarin kwace mota kirar Toyota Corolla. 

Post a Comment

0 Comments