Daga Muhammad Farouk Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami ya bayyana nadamarsa bisa karbar mukamin siyasa da y...
Daga Muhammad Farouk
Ministan sadarwa da
tattalin arzikin zamani, Isa Ali Pantami ya bayyana nadamarsa bisa karbar
mukamin siyasa da ya yi a Nijeriya.
Minista Pantami ya
bayyana hakan ne a wani sakon Bidiyo da MADOGARA ta samu wanda aka
wallafa a shafin YouTube, inda ministan ya nuna damuwarsa bisa wannan hukunci
da ya yanke na dawowa Nijeriya daga Madina domin ya yi wa kasarsa hidima.
Pantami ya ce; “mafi
tsaurin mataki da na dauka a duk duniya a rayuwata zuwa yau shi ne na dawo
Nijeriya daga garin Madina saboda ana bukatar gudummawata a gida. Ban taba
daukar wani mataki a rayuwata da ya ba ni wahala irin wannan ba. Saboda duk
yawon da na yi a duniya, na shiga kasashe birjik, ban taba shiga garin da nake
son sa ba, Allah ya jarabce ni nake son na rayu a cikinsa irin garin Madina ba”,
ya tabbatar.
Minista Isa Ali Pantami
ya ci gaba da cewa; “watarana salloli guda biyar gaba daya a masallacin Manzon
Allah nake yin su. Dukkaninsu guda biyar. ‘Ya’yana masu wayo a masallacin
Annabi (SAW) suke haddar Alkur’ani. Yara a nan suke, iyalanka a nan suke zuwa
su yi sallah. Duk kwana hudu, biyar zuwa shida a karshen mako sai ka je Makkah
ka yi Umarah. Watarana sai karfe daya na dare za ka kama hanya saboda amincin
wurin”, ya tabbatar.
Minista Pantami bai
tsaya nan ba, ya ci gaba da cewa; “kuma abin da ake ba ka na yau da kullum a
matsayin albashi da alawus, wallahil azim ba na iya kashe kashi 25 a cikin 100.
Duk yadda nake jin dadi a wurin, na je Makkah, na sauka a duk sati a Darur
Tauhid ko zamzam ne ko kuma Hilton, bana kashe kashi 25 na abin da ake ba ni. Wahalar
sha’ani shi ne ba inda ya kai gida. Idan kowa ya guji gida, to wa zai zo ya
bayar da gudummawa wajen rage matsalar gidan?” ya tambaya.
Ya ci gaba da cewa; “kuma
duk kasar da ka gani a duniya ‘yan kasar ne suka yi hakuri suka tsaya suka
gyarata. Amma ba a taba gyara wani gari a duniya kowanne dan gari ya ce shi zai
bar garin ya koma wani wuri ya zauna ba. Ba a taba gyara da haka ba”, ya
jaddada.
Minista Pantami har
wala yau a wani bangare na bayaninsa, ya kara da cewa; “dole ne sai an hakura
da wadansu abubuwa. An hakura amma har yanzu ina jin radadin a zuciyata yana
damuna! Har yanzu! Wani lokaci a yanzu haka ko a TV (talabijin) aka nuno Madina,
ana sallah, wallahil azim sai na ji kwalla”, ya lurantar.
Ya kara da cewa; “Rashin
hakuri idan na zauna, da muna da irin ‘group’ na abokan aikinmu da muke zuwa masallaci
mu yi sallah tare, akwai wadansu ‘yan Ingila irin su Abdullahil Na’amun, Dakta
ne, su Dr Muhammad Buna’id, su Dr Ali Tufayl, aminaina ne, kullum zamu fito
daga ofis sai a shiga mota a je harami minti biyar an isa masallaci an yi
sallah an dawo. Kawai da karatu zamu fito mu shiga sallah. Idan na ga sun yi ‘posting’
a ‘group’ sun ce ku sauko mu shiga masallaci, kawai sai ya zama duk abin da
nake sai na gagara, saboda me? Saboda ina tuna wadannan ‘moment’ din, haka na
yi ta zare kaina a ‘group’ din ba zan iya zama ba. Saboda me? Abin da ya fi min
radadi shi ne wannan!”
Har wala yau Pantami ya
nuna yadda a kowanne yini mafi kankantar sallar da suke samu shi ne sau hudu
kowanne wuni, ya ce wani lokacin duka khamsul salawat a masallacin Annabi zaka
yi su; “akwai ribar da ya kai wannan?” ya tambaya.
“gidan da nake zaune
zuwa rijiyar Sayyidina Usman, wanda ya siya Annabi ya ce makomarsa aljanna ne,
ba na kai minti biyu ko uku nake isa wurin. Ina zaune a Faisaliya, anguwar da
nake ga ni ga Jami’a, hanya ce tsakani da Jami’a, idan na koma daya bangaren, kusa
da Jami’a gidan gwamnan Madina ne. Idan ban je harami ba, a nan tare da shi
muke sallah. To ka fito a wannan hali din, ka bar damar ka zo, Allah dai yasa
mu dace. Allah ya karbi wannan a matsayin ibada. Amma ba abu ne mai sauki ba
gare ni har yanzu!” inji Minista Pantami.
Cikakken bayanin cikin bidiyo;
Jarabawa ce malan Allah yabaka ikon cinye ta
ReplyDeleteMalam jarabawa ce. Allah ya san za ka iya Shi yasa ya daura .muna maka fatan alkhairi Kuma Allah ya tsareka da ga dukkan makirci Mai makirci
ReplyDelete