Nijeriya Za Ta Rushe Cikin Wata Shida, Inji Robert Clarke


Daga Muhammad Farouk

Wani babban Lauyan Nijeriya, Robert Clarke, SAN ya ce akwai yiwuwar Nijeriya ba za ta rayu ba nan da wata shida sakamakon matsalar tsaron kasar da ya tabarbare, MADOGARA ta labarto. 

Robert Clarke, ya bayyana hakan ne a hirar da ya yi da gidan Talabijin na Channels a shirinsu na ‘Sunday Politics’ na ranar Lahadi, ya ce Nijeriya ta dauko hanyar rushewa ta kowanne janibi. Wanda ya nusasshe da cewa matsalar tsaron da kasar ke fuskanta ya yi muni fiye da lokacin gwamnatin baya ta Shehu Shagari a 1982. 

Robert Clarke, ya ce; “matsalar Nijeriya shi ne wadanda ya kamata su sani ba su son su sani kuma ba su sani ba. Bangaren tsaro idan banda magana, magana, da kuma magana, me suke yi? Matsalar tsaron kasar a yau ya yi muni, Ni Robert Clarke, ba zan iya tabbatar da cewa ko Nijeriya za ta kara wata shida ba”, ya tabbatar. 

Robert Clarke ya ce; “matsalolin sun yi yawa matuka, ‘yan siyasarnan ne dai suka kirkiri matsalolin tun bayan kundin tsarin mulkin na 1999, wadannan tsoffin ‘yan siyasar wanda suke matasa a wancan lokacin, sun yi nutso cikin kudaden satar Sani Abacha, inda suka kirkiri jam’iyyun siyasa ga kawukansu, suka kuma kwashi kudi suka shiga siyasar, Nijeriya har yanzu ba ta dawo daidai ba”, inji shi. 

Ya ci gaba da cewa; “Nijeriya ta munana fiye da yadda take a 1982. A 1982 lokacin da Shehu Shagari yake shugaban kasa ta fi sauki fiye da yadda Nijeriya take a yau a 2021. Mene ne matsalar? Rashin kyakkyawan shugabanci da bamu da shi!”, ya tabbatar. 

Robert Clarke da yake bayar da shawara kan matsalar tsaron kasar wanda ya ce shekaru bakwai da suka gabata ya yarda da gwamnati da kashi 70 cewa za su iya wani abu dangane da tsaron, amma a cewarsa da yanzu Nijeriya ta dauko hanyar rushewa, imaninsa da gwamnatin bai kai kashi 10 ba. 

“akwai bukatar a yi wani abu; mafita a nan a mahangata shi ne; ya kamata Nijeriya ta sauya daga yadda take a yau, kuma hanyar sauya ta kawai shi ne a sanya dokar ta baci wanda zai sanya daftarin kundin tsarin mulki na 1999 ya zama ba ya aiki. Muna son a kafa dokar ta baci a Nijeriya a yau”, inji shi. 

Sai dai ya yi karin haske cewa; “ya ya zamu yi hakan? A karkashin kundin tsarin mulkin Nijeriya, shugaban kasa, wanda shi ne Babban kwamandan tsaro yana da dukkanin karfin da zai tursasawa shugabannin hafsoshin tsaro. Ya yi magana da shugaban majalisar Dattawa, ya yi magana da Kakakin majalisa, da dukkanin gwamnonin jihohi cewa za a sanya dokar ta baci a kafatanin Nijeriya, wanda ke nufin dukkanin gwamnoni dole su tafi, haka ma ‘yan majalisa”, ya jaddada.  

Ya karkare da cewa; “sai a sanya jagorancin sojoji a dukkanin yankunan siyasa shida da muke da su muka yarda da su su lura da wadannan jihohi, ina mai tabbatar maka, a lokacin da aka maida Nijeriya zuwa jihohi shida, kuma aka sanya dokar ta baci, kashi 80 na kudaden da ake kashewa wajen tafiyar da shugabanci za a dawo da su asusun gwamnati ne. Daga nan sai mu zauna a sake yi wa Nijeriya kwaskwarima, dukkanin jihohi su kula da kudaden da suke samu”, inji shi. 


Post a Comment

0 Comments