Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Nijeriya Za Ta Taimaka Wa Chadi Wajen Tabbatar Da Zaman Lafiya, Inji Buhari

Daga Auwal Adam  Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Nijeriya za ta taimaka wa kasar Chadi domin ganin an tabbatar da zaman laf...


Daga Auwal Adam 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce Nijeriya za ta taimaka wa kasar Chadi domin ganin an tabbatar da zaman lafiya da kuma komawar kasar kan tsarin doka da oda. 

Shugaba Buhari ya dauki alkawarin ne a jiya Juma’a a lokacin da yake ganawa da Shugaban Majalisar Riko ta kasar Chadi Laftanal Janar Mahamat Idris Deby Itno wanda ya ziyarce shi a fadarsa da ke Abuja.

Kakakin shugaban kasar Femi Adesina ne ya tabbatar da hakan a sanarwat da ya fitar jim kadan bayan wannan ganawa, inda ya ruwaito Buhari na cewa ‘’kasashen biyu na da abubuwan da suka hada su, wato al’adu da kuma makwabtaka’’, yana mai cewa ‘’Nijeriya tana sane da muhimmancin irin rawar da Chadi ta taka wajen yaki da ayyukan ta’addanci, kuma kasashen biyu za su ci gaba da wannan alaka a tsakaninsu’’.

Buhari ya bayyana tsohon shugaba Marshal Idris Deby Itno a matsayin “ amininsa sannan kuma cikakken aboki ga Nijeriya da ba za a taba mantawa da irin rawar da ya taka don kare Nijeriya ba.’’

Sanarwar ta kara da cewa Buhari zai bada gudummuwar da ta dace don karfafa Hukumar Raya Tafkin Chadi (LCBC) da kuma jaddada goyon bayan ga Rundanar. 

No comments